Mutum 257 sun mutu a hatsarin jirgi a Aljeriya

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Kalli hoton bidiyon wurin da jirgin ya fadi

Mutum 257sun mutu a hatsarin jirgin soji da ya faru a arewacin Aljeriya, a cewar ma'aikatar tsaron kasar.

Lamarin ya faru ne da jim kadan bayan tashin jirgin daga filin jirgin sama na sojoji da ke Boufarik ksa da Algiers babban birnin kasar. da safiyar Laraba.

Akasarin wadanda suke cikin jirgin sojoji ne da kuma iyalansu ,a cewar ma'aikatar tsaro.

Akawai ma'aikatan jirgi sama 10 da suka mutu a cikin hatsarin jirgin.

Kawo yanzu ba bu cikakken bayani akan abinda ya janyo hatsarin jirgin sama .

Kafar talbijin ta kasar ta ce, motocin daukar marasa lafiya 14 sun isa wajen da lamarin ya afku inda aka dauki wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

Wannan lamari dai ya faru ne a safiyar ranar Laraba a filin jirgin saman soji na Boufarik da ke kusa da babban birnin kasar Algiers.

Hotunan wajen da lamarin da ya afku sun nuna yadda hayaki ke fitowa daga tarkacen jirgin a filin.

Wata sanarwa daga ma'aikatar tsaron kasar ta ce, shugaban rundunar sojin kasar, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike a kan musabbabin afkuwar hadarin, inda kuma zai kai ziyara wajen.

Karin bayani

Kafar yada labarai ta Algerie24, ta ruwaito cewa, fiye da sojoji 200 ne a cikin jirgin.

Yayin da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce mutane da dama sun mutu a cikin jirgin.

Shekara hudu da suka gabata wani jirgi da ya dauki sojoji da iyalansu ya yi hadari a kasar ta Algeria, inda mutum 77 suka rasa rayukansu.

Ana dai yawan samun hadarin jirgin sama a kasashe da dama inda ake kuma asarar rayuka.

Ko a watan Fabrairun 2018 ma, wani jirgin sama ya fadi a yankin Zagros mai cike da tsaunuka a lardin Isfahan a lokacin da yake kan hanyarsa daga Tehran zuwa Yasuj da ke kudu maso yammacin Iran inda mutum 66 suka mutu.

Labarai masu alaka