Yawan 'yan Najeriya ya doshi miliyan 200 - Gwamnati

'Yan Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A kidayar da aka yi ta shekarar 2006 dai yawan al'ummar Najeriya miliyan 140 ne.

Hukumar Kidiya ta kasa NPC ta ce yawan al'ummar Najeriya ya kusa kai wa miliyan 200.

Hukumar NPC ta fitar da wannan sabon adadi ne a ranar Talata a birnin New York na Amurka a wajen taro kan yawan mutane da ci gaba karo na 51.

Shugaban hukumar kidayar Mr Eze Duruiheoma, ya ce a yanzu yawan al'ummar kasar ya kai miliyan 198, wato miliyan biyu ya rage ta kai miliyan 200.

Mista Duruiheoma ya ce ana hasashen cewa Najeriya za ta zama kasa ta uku da ta fi yawan al'umma a duniya nan da shekara 30 masu zuwa.

Ya kara da cewa a shekaru 50 da suka gabata, yawan al'ummar mutanen da ke zaune a birane a kasra ya karu sosai ba tare da samun karin ababen more rayuwa da zai ishe su ba.

A watan da ya gabata ma jakadan Burtaniya a Najeriya Paul Arkwright, ya yi bayyana irin wannan damuwar a wajen wani taro da aka yi a Abuja.

Mr. Arkwright ya yi gargadi cewa za a fuskanci gagarumar matsala saboda aywan al'umma, musamman ganin yadda rashin aikin yi ya yi katutu a tsakanin matasa, ko rashin samun ilimi da kuma rashin ingantattun cibiyoyin lafiya.

A kidayar da aka yi ta shekarar 2006 dai yawan al'ummar Najeriya miliyan 140 ne.

Amma shekara 10 kacal bayan nan, ta zamo ita ce kasa ta bakwai mafi yawan al'umma a duniya, wanda hakan ke nufin cewa daya daga cikin ko wadanne mutum 43 a duniya dan Najeriya ne.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen cewa Najeriya za ta wuce Pakistan da Brazil da Indonesiya da Amurka a yawan al'umma nan da shkerar 2060, ganin yadda yawan al'ummar kasar ke karuwa.

Labarai masu alaka