Algeria plane crash scene footage emerges
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kalli wurin da jirgi ya kashe mutum 250 a Aljeriya

An samu hotunan bidiyo daga wurin da mummunan hadarin jirgin sama ya afku a kasar Aljeriya.

Gidan talbijin na kasar ya nuna hayaki yana fitowa daga baraguzan jirgin.

Lamarin ya faru ne jim kadan bayan da jirgin ya tashi daga filin saukar jiragen soji na Boufarik kusa da babban birnin kasar, Algiers.

Har yanzu ba a son musabbabin hadarin ba.

Motocin agaji sun isa wurin sannan suka debi wadanda suka samu raunuka zuwa asibiti.

Labarai masu alaka