An bukaci a fara kiran sallah ta WhatsApp a Ghana

Musulmai na sallah a dandanyar kasa Hakkin mallakar hoto Getty Images

Al'ummar Musulmi a Ghana sun yi watsi da shawarar da aka bayar na cewa limamai su rinka kiran sallah ta manhajar Whatsapp, inda suka ce abu ne da ba za su "taba yarda ba."

Hakan dai ya biyo bayan kiran da ministan muhalli, kimiyya da fasaha, Farfesa Frimpong Boateng, ya yi cewa ya kamata limamai su ajiye amfani da lasifika wajen kiran sallah, su koma amfani da tura sakon waya ko kiran ta manhajar WhatsApp.

A cewar Ministan, hakan zai rage hayaniya a kasar.

Farfesa Boateng ya ce, 'Me ya sa idan lokacin sallah ya yi ba za a iya sanar da mutane ta sakon wayar salula ko WhatsApp cewa lokacin sallah ya yi ba?

"Ai sai limami kawai ya aika da sako ta WhatsApp ya sanar da mutane cewa kowa ya hallara a masallaci za a yi sallah".

To amma mai magana da yawun babban limamin kasar, a wata tattaunawa da yayi da sashen Turancin Broka na BBC ya yi watsi da kiran, inda ya ce 'Kiran sallah da murya a musulunci al'adace da aka saba wadda aka gada tun kaka da kakanni, kuma wannan abune da ba za mu canja shi ba'.

Wani Musulmi ne a shafin sada zumunta, ya yi suka a kan abin da ministan ya ce, inda ya ce sam bai dace ba.

Labarai masu alaka