Mutum 257 sun mutu a hatsarin jirgi, An bukaci a fara kiran sallah ta WhatsApp

Mutum 257 sun mutu a hatsarin jirgi

Mutum 257sun mutu a hatsarin jirgin soji da ya faru a arewacin Aljeriya, a cewar ma'aikatar tsaron kasar.

Lamarin ya faru ne da jim kadan bayan tashin jirgin daga filin jirgin sama na sojoji da ke Boufarik ksa da Algiers babban birnin kasar. da safiyar Laraba.

Hakkin mallakar hoto AFP

An bukaci a fara kiran sallah ta WhatsApp

Al'ummar Musulmi a Ghana sun yi watsi da shawarar da aka bayar na cewa limamai su rinka kiran sallah ta manhajar Whatsapp, inda suka ce abu ne da ba za su "taba yarda ba."

Hakan dai ya biyo bayan kiran da ministan muhalli, kimiyya da fasaha, Farfesa Frimpong Boateng, ya yi cewa ya kamata limamai su ajiye amfani da lasifika wajen kiran sallah, su koma amfani da tura sakon waya ko kiran ta manhajar WhatsApp.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

An kama mai hada wa Boko Haram bama-bamai

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kama wani mutum da ya shahara wajen hada bama-bamai ga mayakan kungiyar Boko Haram.

Rundunar ta ce an kama Adamu Hassan ne da ake yi wa lakabi da suna 'Baale' a garin Kaltungo na jihar Gombe da ke shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rundunar sojin Nigeria ta ce dakarunta na samun nasarar fatattakar 'yan Boko Haram

'Yawan 'yan Najeriya ya doshi miliyan 200'

Hukumar Kidiya ta kasa NPC ta ce yawan al'ummar Najeriya ya kusa kai wa miliyan 200.

Hukumar NPC ta fitar da wannan sabon adadi ne a ranar Talata a birnin New York na Amurka a wajen taro kan yawan mutane da ci gaba karo na 51.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A kidayar da aka yi ta shekarar 2006 dai yawan al'ummar Najeriya miliyan 140 ne.

Kun san tsoffin jaruman Indiya da har yanzu ke fim?

Mun yi nazari game da tsofaffin jaruman Bollywood mata wadanda suke raye kuma suke ci gaba da taka rawa a fina-finan.

Hakkin mallakar hoto Qoura
Image caption Kamini Kaushal

Cinikin 9mobile: An ba da kafin alkalami

Daya daga cikin masu sha'awar sayen kamfanin sadarwa na 9mobile a Najeriya ya bayar da kafin alkalami dala miliyan 50.

Kamfanin da ya biya kudin shi ne Teleology Holdings, wanda aka baiwa fifiko a cikin wadanda suka nuna sha'awar tasu.

Hakkin mallakar hoto MKM
Image caption Hukumar NCC ta ce abin da ya rage shi ne a ciko dala miliyan 450 nan da kwana 90

Bidiyo: Mutum 257 sun mutu a hatsarin jirgi a Aljeriya

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Fiye da mutum 250 ne suka mutu bayan da wani jirgin soji ya yi hadari a kasar Aljeriya.

Karanta karin wasu labaran

Domin samun karin bayani da kuma tofa albarkacin bakinku a kan wadannan labaran, sai ku garzaya shafinmu na BBC Hausa Facebook.

Labarai masu alaka