Abin da ya sa na nemi wa'adi na biyu - Buhari

buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce maganganun 'yan Najeriya ne suka sa ya bayyana aniyarsa ta sake neman takara karo na biyu a zaben shekara mai zuwa.

Da yake magana a lokacin da ya gana da shugaban mabiyar darikar Anglican Justin Welby, Buhari ya ce yana son ya mayar da hankali wurin bunkasa ayyukan noma da tsaro da tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Ya kara da cewa "Mafiya yawan 'yan Najeriya sun gamsu da irin ayyukan da mu ke yi, shi ya sa nake so na ci gaba da mulki".

A ranar Litinin ne shugaban ya shaida wa jam'iyyarsa ta APC cewa yana sha'awar neman wa'adi na biyu.

Ra'ayoyin 'yan kasar sun sha banban kan sanarwar ta shugaban ya bayar, inda wasu ke cewa bai tabuka abin kirki ba, a don haka bai cancanci a sake zabarsa ba.

Sai dai magoya bayan shugaban na ganin ya taka rawar kirki, kuma babu wanda ya dace ya ci gaba da jan ragamar kasar idan ba shi ba.

A shekara ta 2015 ne Buhari ya zamo dan adawa na farko da ya taba lashe zaben shugaban kasa a Najeriya inda ya kayar da Goodluck Jonathan.

An zabe shi bisa alkawarin yaki da cin hanci da rashawa da kuma bunkasa tattalin arziki da yaki da kungiyar Boko Haram.

Amma masu sharhi da dama na ganin bai cika mafiya yawan alkawuran da ya dauka ba.

Abin da Buhari ya shaida wa Welby

Hakkin mallakar hoto Nigerian Government

"Mun rage shigo da shinkafa da kusan kashi 90%, inda hakan ya sa a ka rage biliyoyin daloli a kudaden da a ke kashewa.

Mutanen da su kai rububin kudin man fetur, a yanzu sun koma noma. Hatta kwararru ma sun koma noma.

Najeriya za ta iya ciyar da kanta kwanan nan. Na ji dadin hakan.

Kan batun yaki da ta'addanci, ya jaddada bukatar ci gaba da ilimantar da mutane, "domin a daina amfani da addini a na yaudararsu," inda ya kara da cewa babu wani addinin gaskiya da ya yadda da kashe mutanen da ba su yi laifin komai ba.

Wa zai iya ja da Buhari a APC?

Hakkin mallakar hoto FACEBOOK/BUHARI SALLAU

Dama dai tun kafin wannan sanarwa wasu masu sharhi su ka fara tofa albarkacin bakinsu kan yiwuwar sake tsayawar Buharin takara.

Malam Jafar Jafar wani mai sharhi ne kan harkokin siyasar Najeriya, kuma ya ce yana ganin duk wani dan siyasa da yake neman takara a jam'iyyar APC yana bata wa kansa lokaci ne kawai, "matukar Shugaba Buhari zai sake yin takara."

Ya ce: "Idan har Buhari zai yi takara, to babu makawa jam'iyyarsa shi za ta tsayar a zaben 2019."

"Kuma da wahala a ce ba zai yi takara ba," in ji shi.

Malam Jafar ya ce zabin da ya rage masu muradin yin takara a jam'iyyar APC shi ne kawai su sauya jam'iyya.

"Ga jam'iyyu nan da yawa. Idan dai ba a yi murdiya ba a zaben 2019, akwai yiwuwar jam'iyyar APC za ta iya faduwa zabe."

"Saboda a gaskiya farin jinin jam'iyyar da na Shugaba Buhari ya ragu sosai."

Bayani kan Shugaba Muhammadu Buhari a takaice:

Hakkin mallakar hoto Photoshot
Image caption Wata mai goyon bayan Buhari na sumbatar hotonsa da aka manna
  • Shekararsa 72
  • An zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 28 ga Maris 2015
  • Ya yi shugaban mulkin sojan Najeriya daga 1984 zuwa 1985
  • An hambare shi a juyin mulki
  • Ya samu shaidar rashin kare hakkin dan adam
  • An yi amanna ba shi da cin hanci da rashawa
  • Mai ladabtarwa ne - a kan sa ma'aikatan gwamnati tsallen kwado idan suka yi lattin zuwa aiki
  • Musulmi ne daga arewacin Najeriya
  • Ya tsallake rijiya da baya a wani hari da Boko Haram ta kai masa