Gaddafi ne ya bai wa makiyaya makamai - Buhari

gaddafi Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya zargi tsohon shugaban Libiya Mu'ammar Gaddafi da bai wa makiyaya makamai a yankin Yammacin Afirka.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Femi Adesina ya aike wa manema labarai a ranar Laraba.

Sanarwar ta kunshi bayanan da shugaban ya yi wa Archbishop na Canterbury Justin Welby ne, a kan dalilinsa na son sake tsayawa takara karo na biyu a ganawar da suka yi a birnin Landan.

Ya bayyana wa Mista Welby cewa rikicin manoma da makiyaya tsohon abu ne da aka dade ana fama da shi a kasar.

"Sai dai a yanzu ya yi muni ne saboda yadda 'yan bindiga daga yankin kudu da hamadar sahara ke kara kutsawa cikin yankin Yammacin Afirka," in ji shugaban.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Makiyaya da a baya mu ka san su da daukar sanda don gyara hanyar wucewarsu kawai, amma a yanzu su na daukar mugayen makamai in ji Buhari

Shugaba Buhari ya kara da cewa: "Mu'ammar Gaddafi na Libiya ne ya horar da wadannan 'yan bindiga. Da aka kashe shi kuma sai suka tsere da makamansu.

"Mun ga ire-irensu a yakin da muke yi da Boko Haram. Makiyaya da a baya mu ka san su da daukar sanda ko lauje don gyara hanyar wucewarsu kawai, amma wadannan na yanzu su na daukar mugayen makamai."

Shugaban Najeriyar ya kuma cewa Archbishop na Canterbury din matsalar rikicin manoma da makiyaya ba abun da ya shafi addini ba ne, lamari ne da ya shafi zamantakewa da tattalin arziki, ''amma muna aiki don samar da mafita."

Ya koka da cewa "siyasa marar kan gado" ce ta jawo rikicin manoma da makiyaya, amma ya bayar da tabbacin samar da mafita ta din-din-din.

A bara, gwamnatin Najeriya ta sanya dokar hana kiwo a wasu yankunan kasar wacce ta jawo ce-ce-ku-ce, inda ta ce a dinga killace shanu a waje daya.

Sai dai kuma an yi biris da wannan doka kuma ana ci gaba da samun rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya a fadin kasar.

Rikicin manoma da makiyaya

Rikicin manoma da makiyaya dai a Najeriya ya yi sanadin asarar rayuka daga dukkan bangarorin biyu, al'amarin da ya jawo hankalin kusan daukacin 'yan Najeriya.

Rikicin ya fi kamari ne a jihohin Filato da Benue da Taraba da Nassarawa da Kaduna.

Hakkin mallakar hoto AFP

A baya gwamnatin tarayya ta yi kira ga gwamnonin jihohin da lamarin ya shafa su samar da wuraren kiwo.

Sai dai gwamnonin sun yi fatali da wannan kira, suna masu cewa ba su da isassun filayen da za su bayar domin kiwo.

Amma a watan Fabrairu Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya gayyaci Fulani makiyaya su koma jiharsa domin gudanar da kiyo ba tare da samun matsala ba.

Karanta karin wasu labarai: