Alkalin wasa ne ya zalunce mu – Buffon

Gianluigi Buffon da Michael Oliver Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An bai wa Gianluigi Buffon jan katinsa na farko a gasar zakarun Turai

Kyaftin din Juventus Gianluigi Buffon ya ce alkalin wasa ya zalunce su a wasan da Real Madrid ta fitar da su daga gasar cin kofin zakarun Turai.

Alkalin wasan na Ingila Mark Oliver ya bai wa Madrid fanareti a mintin karshe bayan da Mehdi Benatia ya ture Lucas Vazquez, sannan kuma ya bai wa Buffon jan kati.

"A zahiri take cewa fanaretin boge ne. Babu tabbas," kamar yadda Buffon ya shaida wa kafar yada labaran Italiya.

Buffon ya kara da cewa kamata ya yi Oliver ya "zauna a cikin 'yan kallo ya ci dankali saboda yadda ya lalata mana burinmu".

Real ta samu nasara da ci 3-0 a wasan farko amma sai Juventus suka rama a wasa na biyu, inda Mario Mandzukic ya ci biyu sannan Blaise Matuidi ya ci ta uku.

Sai dai a lokacin da ake shirin tafiya karin lokaci, sai Oliver ya bai wa Madrid fanareti.

Kuma Cristiano Ronaldo ya narka kwallon a cikin raga a minti na 97.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cristiano Ronaldo ya zura kwallo 41 a Real Madrid a kakar bana

Buffon ya zake wurin nuna bacin ransa abin da ya sa aka ba shi jan katinsa na farko a gasar zakarun Turai a wasansa na 650 a Juventus.

Kyaftin din na Juventus ya ce babu yadda za a ce wannan fanaretin gaske ne.

Real Madrid da Liverpool da Roma da kuma Bayern Munich ne suka kai zagayen kusa da na karshe.

A ranar Juma'a ne za a raba kungiyoyin da za su kara da juna.

Labarai masu alaka