Hotunan abubuwan da suka faru a makon nan

Wasu daga cikin hotuna mafi kyau na abubuwan da suka faru a Afrika da wasu wurare a makon nan.

Mata' yan Afriika kudu suke sarawa yayin da suke maci kusa da gidan Winnie Mandela a Soweto da ke Johannesburg a ranar 8 ga watan Afrilu na shekarar 2018. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu mata 'yan Afrika ta kudu suke sarawa yayin da suke maci a ranar Juma'a kusa da gidan marigayayi Winnie Madikizela Mandela mai fafitukar kawar da mulkin wariyar launin fata , wadda ta rasu a ranar 2 ga watan Afrilu.
Wasu mata dalibai na cin abinci ya yinda wasu mata da ke sanye da rigunan jam'iyyar ANC sun tsaya a filin wasa na Orlando da ke Soweto a birnin Johannesburg a ranar 11 ga Afrilu , 2018. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar Laraba , mutane sun taru a filin wasa na Orlando da ke Soweto domin halatar taron adu'oin tunawa da Winnie Madikizela-Mandela
Wata da ke goyon jam'iyyar ANC a taron adu'oi na Winnie Madikizela-Mandela a filin wasa na Orlando a garin Soweto da ke Johannesburg a kasar Afrika ta kudu a ranar 11 ga watan Afrilu 2018. Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Magoya bayanta da dama sun dauke ta a matsayin 'uwa kuma suna kiranta" Mama Winnie".
Clementine Meukeugni Noumbissi a zagayen karshe na gasar daukar nauyi na kilo 90 na mata a wasannin Commonwealth da ake yi a Gold coast a ranar 9 ga watan Afrilu 2018. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yar kasar Kamaru Clementine Meukeugni Noumbissi ta yi murna a ranar Litini bayan ta sami tagulla a gasar daukar nauyi na mata na kilo 90 a wasannin Commonwealth da ake yi a Ostreliya .
Grace Legote na fafatawa a wasan lankwasa jiki na karshe a gasar wasannin commonwealth da ake yi a Gold Coast a ranar 12 ga watan Afrilu 2018 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Grace Legote 'yar kasar Afrika ta kudu a wasan masu lankwasa jiki na karshe a ranar Alhamis. Ta sha kaye a hannun Cyprus da Canada da kuma Malaysia wadanda suka samu lambobin zinari da azurfa da kuma tagulla.
Isaac Makwala 'dan kasar Botswana ya rika murna lokacin da ya tsallake layi na karshe bayan ya yi nasara a wasanin guje-guje na maza na mita 400 a gasar Commonwealth da ake yi Gold coast a filin wasa Carrara a ranar 10 ga watan Afrilu . Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Isaac Makwala dan kasar Botswana ya lashe wasan guje -guje na mil 400 a ranar Talata kuma yana farin ciki da yin haka.
Masu fafatawa sun kai zagaye na uku a gudun famfalaki karo 33 tsakanin Rich Mbirika da Nord El Maharch a kudancin Morroco a cikin sahara a ranar 10 ga watan Afrilu , 2018 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A wannan rana a Morroco, aka yi gasar gudun famfalaki na kwanakin shida a cikin sahara.
Wani matashi mai hakar ma'adinai a mahakar gwal ta Makala da ke kusa da garin Mongbwalu da ke lardin Ituri ,a gabashin jamhuriyar Dimukradiyar Congo, a ranar 7 ga watan Afrilu, 2018. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani ma'aikaci mai hakar ma'adinai ya rataya jaka mai nauyi a ranar Asabar a Mongbwalu da ke gabashin Jamhuriyar Dimukradiyar Congo.
Wata yarinya mai tabo a fuska a sansanin Bunia , da ke lardin Ituri,a gabashin jamhuriyar Dimukradiyar Congo a ranar 9 ga watan Afrilu na shekarar 2018. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A wannan yanki, akwai wata yarinya mai shekara biyu wadda mayakan sa-kai suka raunata, na zaman jira a sansanin da aka tilasta wa mutane barin gidajensu . Shaidu sun ce an kashe mahaifiyarta kuma an datse wa kanwarta hannu a harin da akai wa kauyensu.
Mutane sun taru a taron gangamin da aka shirya wa sabon fira ministan Habasha a garin Ambo mai nisan kilomita 120 da Addis Ababa a ranar 11 ga watan Afrilu 2018. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan Habasha na dakun zaman jiran sabon firaministan kasar, Abiy Ahmed ya zo ya yi mu su jawabi a garin Ambo a ranar Laraba .
Maza a kan dawakai a garin Ambo da ke kasar Habasha a ranar Laraba 11 ga watan Afrilu 2018. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu da suke halartar taron gangami na yankin Oromiya, wanda shi ne matattarar masu zanga zangar nuna adawa da gwamnati, sun iso akan dawakai.
'Yan Habasha sun rike kyandira ya yinda suke halatar taron adu'oi a cocin Holy Trinity Cathedral Orthodox da ke Addis Ababa - a ranar Asabar 7 April 2018 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An gudanar da bikin easter na kiristoci mabiya darikar orthodox ta mazan-jiya. 'Yan Habasha a birnin Addis Ababa sun hallara a coci a ranar Asabar domin yin adu'o'i.
Wata mata na nuna rashin jin dadinta a kusa da sojojin MDD lokacinda mazauna unguwar PK5 inda musulmi suka fi rinjaye suka yi zanga zanga a gaban ofishin MDD a Bangui, da ke jamhuriyar tsakiyar Afrika a ranar 11 ga waatan Afrilu, 2018. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata mata tana zanga zanga a jamhuriyar tsakiyar Afrika a ranar Laraba, yayin da masu zanga zanga suka ajiye gawawwaki 17 a gaban ofishin MDD, inda mamatan fararen hula ne da suka rasa rayukansu a arangamar da aka yi.
Wata mata ta hau kan babur a kasuwar Wurukum da ke jihar Binuwe a ranar Laraba 11 ga watan Afrilu 2018 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wata mata ta hau kan babur tana tafiya a cikin wata kasuwa da ke garin Makurdi da ke Najeriya a jihar Benue.
Ma'aikata sun dibi kasa daga bakin kogin Binuwe a ranar Laraba 11 ga watan Afrilu, 2018. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu aikin kwadago a jihar sun dauki 'kasa da ake amfani da ita wajan gine-gine wadda aka tono daga bakin kogin Benue.

Hotuna daga AFP, Getty Images da Reuters

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC