Rasha za ta harbo makaman linzamin Amurka a Siriya

Wani sojan kasar Rasha Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rasha tana goyon bayan Siriya kuma tana taimakawa gwamnatinta

Rasha ta gargadi Amurka cewa kaddamar da hare-hare kan Siriya bisa zargin amfani da makami mai guba zai iya haifar da yaki tsakanin kasashen biyu.

"Babban abun da ke gaman mu shi ne kawar da yiwuwar yaki," in ji jakadan Rasha a majalisar dinkin duniya Vassily Nebenzia.

Ya zargi Amurka da sa zaman lafiyar duniya cikin hadari, ya kara da cewa halin da ake ciki ya kasance "mai hadarin gaske".

Ana tunanin kasashen Yamma su na shirya kai hare-haren sama kan Siriya, amma Rasha, wacce ta ke mara wa Siriya baya ba ta amince da matakin ba.

"Abin takaici shi ne hakika komai zai iya faruwa" kamar yadda Mr Nebenzia ya shaida wa manema labarai bayan ganawar sirri ta kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York.

Ya ce akwai fargabar cewa abubuwa "za su cakude" saboda akwai sojojin Rasha a Siriya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugabannin Kasashen Yamma suna shirin mayar da martani kan harin makamai masu guba da aka kai ranar Asabar

Manya jami'an Rasha ciki har da na soji, sun yi gargadin cewa za a harbo makamai masu linzami na Amurka da kuma wuraren da aka kaddamar da su idan har aka kai wa ma'aikatan Rasha hari.

Mr Nebenzia ya kuma bukaci kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya sake ganawa a ranar Juma'a don tattauna yiwuwar farmakin sojin da kasashen Yammacin Turai ke shirn kaddamarwa.

Fadar White House ta ce tana ci gaba da duba bayanan sirri kuma tana magana da kawayenta a kan yadda za su mayar da martani a kan amfani da makami mai guba.

A gefe guda kuma, Hukumar da ke kula da hana bazuwar makamai masu guba (OPCW) ta ce masana za su je Siriya dan gudanar da bincike a ranar Asabar.

Labarai masu alaka