Saraki ko Kwankwaso: Wa zai iya ja da Buhari a APC?

Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto JUSTIN TALLIS
Image caption An zabi Muhammadu Buhari ne bisa alkawarin samar da tsaro da yaki da cin hanci da rashawa

Masu iya magana kan ce "sawun gwiwa ya take na rakumi" a duk lokacin da suka yi kokarin kwatanta karfin wani abu ko mutum kan abokan karawarsa, da kuma nuna yadda ya yi musu fintinkau ko kuma zai iya share su ya wuce ba tare da wata matsala ba.

Irin wadannan kalaman su ne suka rinka fitowa daga bakin wasu magoya bayan Shugaba Muhammadu Buhari jim kadan bayan da ya sanar da aniyarsa ta fito takara a zaben 2019 domin yin tazarce.

Masu irin wannan ra'ayi na ganin cewa ba wai kawai a jam'iyyar APC ba, har ma a sauran jam'iyyun kasar, babu wanda zai iya ja da shugaban, kuma duk wanda ya yi yunkurin hakan, to ba zai kai labari ba.

Wannan ya kara fitowa fili bayan da a hirarsa da BBC, Sakataren jam'iyyar na kasa, Alhaji Mai Mala Buni, ya ce sun yi farin ciki matuka da fitowar shugaban, kuma da ma abu ne da suka dade suna jira.

Ko ba komai, wasu za su fassara kalaman nasa a matsayin nuna son kai, da kuma hasashen cewa ba za a yi wa sauran 'yan takara adalci ba. Duk da cewa kawo yanzu babu wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar a cikin 'ya'yan jam'iyyar.

Sai dai an dade ana hasashen cewa akwai wadanda suke shinshina kujerar ta Shugaba Buhari. Kuma wasu na ganin za su iya yin kukan-kura su fito ko da kuwa za a dora musu karan tsana - kuma ba za su kai labari ba.

Irin haka dai ya taba faruwa ga tsohon mataimakin Shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar, wanda ya kalubalanci Goodluck Jonathan a jam'iyyar PDP a 2011, duk da cewa Mr Jonathan din shi ne shugaban kasa kuma yana samun goyon bayan shugabanni da gwamnonin jam'iyyar.

Wa zai iya kukan-kura a APC

Jam'iyyar APC dai jam'iyya ce ta hadaka - kuma akwai bangarorin da suke ganin ana mayar da su saniyar-ware a tafiyar da ake yi.

Alal misali ana ci gaba da takun-saka tsakanin 'yan tsohuwar jam'iyyar PDP da kuma wasu 'yan majalisun tarayya da gwamnati a gefe guda.

Abin da ya sa ake ganin 'yan majalisar na kokarin sauya fasalin tsarin zaben kasar domin nema wa kansu mafita, amma sun ce suna yi ne domin inganta tsarin dimokuradiyya.

Sanata Bukola Saraki

Hakkin mallakar hoto PIUS UTOMI EKPEI
Image caption Wasu na ganin Bukola Saraki ka iya taka wa Buhari burki

Ana ganin Shugaban Majalisar Dattawa kasar Sanata Bukola Saraki zai iya kalubalantar Shugaba Buhari, ko da yake a halin yanzu ya musanta hakan.

Amma a baya sau biyu yana neman tsayawa takarar shugabancin kasar.

Gogaggen dan siyasa ne kuma yana da goyon baya a tsakanin 'yan majalisun kasar na APC da kuma PDP.

Babban kalubalen da zai fuskanta shi ne irin bakin jinin da ya ke da shi a tsakanin magoya bayan Shugaba Buhari, wadanda suke ganinsa a matsayin wanda yake adawa da shugaban.

Duk da cewa Sanata Saraki ya sha musanta hakan.

Na kusa da shi na korafin cewa ba a tafiya da shi yadda ya kamata duk da rawar da ya taka wurin kafa jam'iyyar APC da kuma samun nasarar Shugaba Buhari.

A don haka ake ganin zai iya neman kujerar shugaban, ko kuma ya fice daga jam'iyyar.

Sanata Rabi'u Musa Kawankwaso

Har ila yau, a zauren majalisar dattawan kasar, akwai Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda shi ma ya taba neman shugabancin kasar a 2015 amma Buhari ya kayar da shi a zaben cikin gida na APC.

Ko da yake a wannan karon bai bayyana aniyyarsa ba tukunna, amma alamu na nuna cewa har yanzu bai hakura ba, kuma watakila ya kara gwada sa'arsa.

Tsohon gwamnan jihar Kanon shi ne ya zo na biyu a zaben fidda gwani na 'yan takarar neman shugabancin a jam'iyyar APC a zaben 2015.

Ya ci gaba da yada akidarsa ta Kwankwasiyya a ciki da wajen Kano. Sai dai ba shi da karbuwa sosai a Kudancin kasar, abin da ake ganin zai iya ba shi matsala.

Haka zalika rikicin da yake yi da mutumin da ya gaje shi, Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje, ya sa karfinsa ya ragu a jam'iyyar a jihar Kano.

Wasu na ganin zai iya yin kukan-kura ya kalubalanci Buhari ko dan ya nuna karfin imaninsa ga tsarin dimokuradiyya.

Ko za su kai labari?

Masana da dama na ganin fitowar Buhari ta rufe kofa ga sauran 'ya'yan APC, ko kuma ba za su iya kai labari ba ko da sun fito.

Duk wani dan siyasa da yake neman takara a jam'iyyar APC yana bata wa kansa lokaci ne kawai matukar Shugaba Buhari ya fito, a cewar Malam Jafar Jafar, wani mai sharhi kan harkokin siyasar Najeriya.

Ya ce: "... babu makawa jam'iyyarsa shi za ta tsayar a zaben 2019."

Malam Jafar ya ce zabin da ya rage masu muradin yin takara a jam'iyyar APC shi ne kawai su sauya jam'iyya.

Ya kara da cewa "Ga jam'iyyu nan da yawa. Idan dai ba a yi murdiya ba a zaben 2019, akwai yiwuwar jam'iyyar APC za ta iya faduwa zabe."

"Saboda a gaskiya farin jinin jam'iyyar da na Shugaba Buhari ya ragu sosai."

Mai fashin bakin ya ce abin da ya sa manyan 'yan siyasar kasar ba su fito sun bayyana aniyarsu ta takara ba, "shi ne kamar wata dabara ce suke don su fito tashi guda idan lokacin fara yakin neman zabe ya yi."

'Yan kasar dai sun zuba ido su ga jerin mutanen da za su fito su bayyana aniyarsu ta neman kuri'unsu musamman bayan da Shugaba Buhari ya bayyana tasa aniyar.

Bayani kan Shugaba Muhammadu Buhari a takaice:

Hakkin mallakar hoto Photoshot
Image caption Wata mai goyon bayan Buhari na sumbatar hotonsa da aka manna
  • Shekararsa 72
  • An zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 28 ga Maris 2015
  • Ya yi shugaban mulkin sojan Najeriya daga 1984 zuwa 1985
  • An hambare shi a juyin mulki
  • Ya samu shaidar rashin kare hakkin dan adam
  • An yi amanna ba shi da cin hanci da rashawa
  • Mai ladabtarwa ne - a kan sa ma'aikatan gwamnati tsallen kwado idan suka yi lattin zuwa aiki
  • Musulmi ne daga arewacin Najeriya
  • Ya tsallake rijiya da baya a wani hari da Boko Haram ta kai masa