An kai mummunan hari sansanin MDD a Mali

Dakarun Minusma a Mali Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kakakin rundunar tabbatar da tsaro ta Majalisr Dinkin Duniya a Mali ya ce, harin babba ne kuma mai daure kai

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an hallaka wani sojinta na wanzar da zaman lafiya, tare kuma da raunta wasu da dama a wani gagarumin hari da aka kai a sansanin dakarunta da ke wajen garin Timbuktu na Mali.

Wani mazaunin garin ya ce gidaje sun girgiza a garin na Timbuktu kuma an ji karar fashewar bama-bamai kusan goma daga nisan kilomita biyar kudu da birnin daga sansanin.

Mai magana da yawun rundunar sojin ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali, Minusma a takaice, ya rubuta a shafinsa na twitter cewa, harin babba ne kuma mai daure kai.

An kai harin ne da manyan makamai da ake harbawa daga nesa da musayar wuta ta fito-na-fito, sannan kuma da motocin kunar bakin-wake biyu.

Rahotanni da dama sun ce daya daga cikin motocin an yi ma ta fentin sojin Mali na kasa, sannan kuma dayar an yi ma ta fenti irin na motocin sojin na Majalisar Dinkin Duniya.

Daya daga motocin biyu ta tashi da bama-baman da ke cikinta a daidai wani wuri da masu gadin sansanin suke.

An kuma ruwaito cewa titin saukar jirgin sama na iyafot din sansanin ya yi mummunar lalacewa a sakamakon farmakin.

An tura dakarun tabbatar da zaman lafiya a arewacin kasar ta Mali tun shekara ta 2013 bayan da mayakan kungiyoyin masu ikirarin Jihadi irin su Al Qaeda suka karkata zuwa can.

Aikin wanzar da zaman lafiyar na Mali ya kasance mafi hadari a duniya.

Labarai masu alaka