'Yawan shan barasa na rage tsawon rai'

Masu shan barasa a Turai Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wani bincike ya ce shan giya fiye da kima na iya rage yawan shekarun rayuwar mutum.

Binciken da aka gudanar a kan ma su shan barasa 600,000 ya nuna cewa shan kofin barasa sau 10 zuwa 15 a mako zai iya rage rayuwar mutum daga shekara daya zuwa biyu.

Haka kuma mutanen da ke shan barasa sama da kofi 18 a mako za su iya hasarar shekaru hudu zuwa biyar na rayuwarsu kamar yadda binciken wanda wasu masana kimiya suka gudanar a Birtaniya ya nuna.

Kundin tsarin shan barasa na Birtaniya na 2016 ya bayar da shawarar cewa kada a wuce shan kofin barasa bakwai a mako daya.

Masanan sun ce sakamakon bincikensu ya tabbatar da shawarwarin da ke cikin kundin tsarin shan barasar na Birtaniya.

Amma masanan sun ce ba su samu karin hadarin mutuwa sakamakon shan barasa a bincikensu ba.

Masana kimiyar wadanda suka kwatanta dabi'un lafiyar masu shan barasa a kasashe 19, sun diba yawan rayuwar da mutum zai iya hasara idan ya ci gaba da shan barasa daga shekara 40 har zuwa karshen rayuwarsa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masana kimiyya sun ce bincikensu ya kalubalanci ra'ayin cewa shan barasa yana da kyau ga lafiya.

Bincikensu ya gano cewa mutanen da suka sha kofin barasa daga biyar zuwa 10 a mako daya za su iya rage watanni kusan shida na rayuwarsu.

Sakamakon binciken ya kuma gano cewa yawan shan barasa na haifar da cututtukan da suka shafi bugun zuciya da mutuwar sassan jiki da kuma hawan jini.

Ana alakanta shan barasa da rage hadarin kamuwa da cututtukan da suka shafi zuciya, amma masana kimiya sun ce wasu nau'in cututtuka da ake kamuwa da su sakamakon shan barasa sun kawar da amfaninta ga ciwon zuciya.

Labarai masu alaka