Hotunan bikin Maulidin Shiekh Ibrahim Nyass a Abuja

Hakkin mallakar hoto @aminugamawa
Image caption Dubun dubatar musulmi mabiya darikar Tijjaniyya daga kasashen Afirka daban daban ne suka halarci taron Mauludin Sheikh Ibrahim Nyass a Abuja.
Hakkin mallakar hoto @aminugamawa
Image caption An gudanar da taron ne a dandalin Eagle Square da ke tsakiyar birnin Abuja.
Hakkin mallakar hoto @aminugamawa
Image caption Mauludin shi ne karo na 32 da aka gudanar a Najeriya domin tunawa da Sheikh Ibrahim Nyass.
Hakkin mallakar hoto Usman S Nafaransa/Facebook
Image caption Babban malamin darikar Tijjaniya a Najeriya Shiekh Dahiru Bauchi tare da ministan Ilimi Malam Adamu Adamu wanda ya wakilci shugaba Muhammadu Buhari.
Hakkin mallakar hoto Emty hart/Facebook
Image caption Maulidin ya kunshi bikin murnar zagayowar haihuwar Shiekh Nyass shekaru 118.
Hakkin mallakar hoto @meandmyearth
Image caption Darikar wadda Wani malami Sidi Ahmad Tijjani ya assasa a shekarar 1784 a Algeria tana daya daga cikin darikun addinin musulunci mafi yawan mabiya a yammacin Afirka.
Hakkin mallakar hoto @FCTWatch
Image caption An toshe hanyoyi da ke zuwa Babban masallacin Juma'a a Abuja zuwa dandalin Eagle Square saboda maulidin.
Hakkin mallakar hoto @kbadtweet
Image caption Mabiya darikar Tijjaniya sun yi imani da yi wa waliyai hidima da nufin samun kusanci ga Allah da kuma neman samun ceton waliyan.
Hakkin mallakar hoto @KwankwasoRM
Image caption Tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na cikin manyan 'yan siyasar Najeriya da suka halarci Maulidin da aka kammala a ranar Asabar.

Labarai masu alaka