Jaruman Indiya maza da suka fi daukar kudi a 2018

1. Salman Khan

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Bayan ya yi manyan fina-finai da suka samu karbuwa kamar Sultan da Bajrangi Bhaijaan, yanzu Salman Khan na cajin kudi 55-60 crore a kowanne fim, kwatankwacin dala miliyan fiye da takwas.

Hakan ya sa ya zamo jarumin da ya fi sauran jarumai karbar kudin fim a 2018.

Fina finan Salman da suka yi fice sun hadar da Maine Pyaar Kiya da Saajan da kuma Hum Aapke Hain Kaun.

2. Aamir Khan

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Jarumin da ke son ganin anyi komai tsari. Aamir Khan na cajar kudi 50 crore a kowanne fim, kwatankwacin dala miliyan fiye da shida.

Lagaan da Dil da Qayamat Se Qayamat Tak.

3. Shahrukh Khan

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Jarumin Bollywood din da har yanzu ake ya yi. Abinda ya ke samu a kan kowanne fim shi ne crore 45, kwatankwacin dala miliyan shida da 100,000.

Yawancin mutane daga kasashen duniya na son fina-finansa.

Manyan fina-finan sa sun hadar da Dilwale Dulhania Le Jayenge da Dil Toh Pagal Hai da kuma Kuch Kuch Hota Hai.

4. Akshay Kumar

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Jarumin da ake yi wa lakabi da Khiladin Bollywood. Ya na taka muhimmiyar rawa a fina-finan kasar India a tsawon shekara 27 da ya yi yana fim.

Wasu daga cikin manyan fina-finansa sun hadar da Rowdy Rathore da Main Khiladi Tu Anari da kuma Mohra.

Yana cajar crore 40 a kowanne fim, kwatankwacin dala miliyan biyar.

5. Hrithik Roshan

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Jarumin da aka sanshi da iya rawa. Ya yi fina-finai da suka yi fice a Bollywood kamar Kaho na Pyar Hai da Koi Mil Gaya da kuma Kabhi Khushi Kabhie Gham.

Yana karbar crore 35-40, kwatankwacin dala miliyan fiye da hudu ke nan.

6. Ajay Devgan

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ya yi suna wajen yin fina-finan fada da na soyayya. Ya yi fina-finai da suka hadar da Phool Aur Kaante da Diljale da kuma Singham.

Yana karbar 22-25 crore, kwatankwacin dala miliyan uku da dubu dari uku.

7. Ranveer Singh

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Yana daga cikin matasan jaruman India da ke tashe a yanzu, saboda fina-finan da ya yi da suka yi fice kamar Ram-Leela da Bajirao Mastani da kuma Padmaavat.

Ya na karbar 20 crore a kowanne fim, kwatankwacin kusan dala miliyan uku ke nan.

Labarai masu alaka