Da gaske ne Shehu Ibrahim Nyass ya bayyana a Maulidin Abuja?

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Tabbas ana ganin Shehu Ibrahim - Dahiru Bauchi

Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron jawabin Shaikh Dahiru Bauchi kan batun:

Batun bayyanar Shehu Ibrahim Nyass ko akasin haka a lokacin da aka yi bikin tunawa da ranar haihuwarsa a wasu biranen Najeriya na ci gaba da haifar da zazzafar muhawara a tsakanin wasu al'ummar Musulmi.

Wasu da dama daga cikin wadanda suka halarci bikin maulidin a Abuja, babban birnin Najeriya da kuma Kaduna, sun ce sun yi ido biyu da babban malamin na darikar Tijjaniya, wanda ya rasu kimanin shekara 43 da ta gabata.

Irin wadannan mutane sun ce sun ga Shehin nasu a siffar da suka san shi ko kuma kamar yadda ya saba bayyana a hoto.

Dubun dubatar mutane ne, maza da mata suka halarci bikin wanda ake yi duk shekara daga sassan kasar daban-daban.

Wani da ya yi ikirarin cewa ya yi tozali da Sheikh Nyass a Abuja, ya shaida wa BBC cewa wani haske ya gani, "sannan sai hoton Shehu ya bayyana".

"Kawai sai na ji gabana ya fadi... kamar inuwar hoto ce take juya wa, ba ya motsi," a cewar Alkasim Tanimu Dutsan Kura daga jihar Katsina.

Ya kara da cewa "Wallahi shi na gani... a maulidin Katsina ma na ganshi da irin wannan kwagirin nasa".

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Yadda na ga Shehu Ibrahim Nyass da idona a Abuja

Ko da gaske ne an ga Shehu a wurin maulidin?

Ba yau aka fara cewa an ga Shehu a wurin Maulidi ba a Najeriya. Kuma bayanan da Alkassim ya yi cewa ya ganshi bara a Katsina sun kara tabbatar da haka.

Sheikh Dahiru Bauchi, na daga manyan almajiran Shaikh Ibrahim Nyass, kuma ya shaida wa BBC cewa bayyanar Shaikh Nyass a wurin maulidin "karama ce" wacce Allah ya ke bai wa waliyyansa.

Ya kara da cewa hakan ba wani abin mamaki ba ne domin a nuna wa mutane cewa karamar waliyyai gaskiya ce.

Shehin malamin, wanda shi ne ya jagoranci maulidin da aka yi a Abuja, ya ce "ana iya ganinsa a ko'ina. A daki ma wadansu sun sha ganinsa, ya kan bayyana haka kawai, wannan ba abin mamaki ba ne, karama ce kawai".

Ya kara da cewa su waliyyai suna iya yin abubuwan da sauran mutane ba za su iya yi ba.

Hakkin mallakar hoto Usman S Nafaransa/Facebook
Image caption Maulidin ya samu halattar jama'a da dama ciki har da Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu wanda ya wakilci Shugaba Muhammadu Buhari

Wasu na da ja kan yiwuwar ganin Shehu

Jama'ar Musulmi musamman a Arewacin Najeriya sun rinka tafka muhawara a shafukan sada zumunta kan wannan batu da ma sauran batutuwan da suka faru a wurin wannan maulidi.

Kuma babu shakka wannan lamari zai ci gaba da jawo ce-ce-kuce musamman ganin cewa akwai wasu manyan malaman addinin Musulunci da ke da ra'ayin cewa babu yadda mutumin da ya mutu zai tashi ballantana har ya sake bayyana a duniya.

Da dama daga cikin mabiya tafarkin Salaf na da irin wannan ra'ayi, kuma sun dade suna fafatawa da 'yan darika a kan batun.

Sai dai wasu mabiya darikar ta Tijjaniya na cewa ba wai Shehun ne yake zuwa da kansa ba, illa dai kawai haskensa ake gani.

Yayin da wasu kuma ke jaddada cewa su ma hakika Shehin suke gani, domin matsayinsa na walittaka ne ya ba shi wannan daraja.

Image caption Tijjaniya na da mabiya sosai a Najeriya

Bayani kan darikar Tijjaniya

Hakkin mallakar hoto Getty Images
 • An kafa darikar ne a kasar Aljeriya a shekarar 1784
 • Sheikh Ahmad ibn Muhammad al-Tijjani ne ya kafa ta
 • Ta yadu zuwa sassan duniya daban-daban, inda ta ke da mafi yawan mabiyanta a Arewaci da kuma Yammacin Afirka
 • Tana kuma da karin mabiya a Afirka Ta Kudu, da Indunisiya da kuma sauran sassan duniya
 • Akwai sauran dariku na Sufaye a addininin Musulunci amma Tijjaniya ta fi kowacce girma
 • Sun ce suna da muhimman ayyukan ibada guda uku a kowace rana:
 • Neman gafarar Allah; Yin salati ga Annabi Muhammad (SAW) da kuma kadaita Allah
 • Sai dai ana zarginsu da wuce gona da iri wurin nuna soyayya ga Shehunnansu, lamarin da wasun su ke musanta wa
 • Ana alakanta Sheikh Ibrahim Nyass da farfado da darikar a karni na 20 bayan ta kwanta dama
 • An haife shi a kasar Senegal kuma jama'a kan yi tattaki daga sassan nahiyar da dama domin ziyartar kabarinsa
 • Darikar Tijjaniya ta kasu kashi-kashi musamman a kasashe irin su Najeriya inda suke da mabiya sosai

Labarai masu alaka