Syria ta harba bindigogin kakkabo jirgin sama

Shugaba Assad na amfani da wannan lokaci ya nuna musu cewa yana nan da karfinsa Hakkin mallakar hoto Associated Press
Image caption Shugaba Assad na amfani da wannan lokaci ya nuna musu cewa yana nan da karfinsa

Kafar watsa labarai ta Syria ta bayar da rahoton cewa an harba bundugogin kakkabo jirgin sama a wani martani na harin makamai masu linzami da aka kai sansanin sojin sama na Shayrat wanda ke kusa da birnin Homs.

Akwai kuma rahotannin da ba a tabbatar ba da ke cewa an tare wasu makaman masu linzami da aka harba sansanin sojin sama na Dumair wanda shi kuma yake kusa da Damascus.

Dukkanin waddannan rahotanni na hare-haren na makamai masu linzami da aka nufa kan cibiyoyin sojin na Syria babu wani tartibin bayani na daga inda aka harba makaman ya zuwa yanzu.

Hedikwatar tsaron Amurka, Pentagon, wadda ta jagoranci kai hare-haren hadin gwiwa na makamai masu linzami kan Syriar tsakaninta da Faransa da Birtaniya a matsayin hukuncinta na kai hari da makamai masu guba, Amurkar ta ce ba wani hari da ta kai a wannan lokacin a wadannan yankuna.

A makon da ya gabata an zargi Isra'ila da kai hari na makami mai linzami kan sansanin sojin sama na T-4 na Syriar.

A wannan karon, Israila ba ta ce komai ba, ballantana a san ita ta kai su wadannan hare-haren na yanzu.

Yayin da duk ake wannan ma'aikatar harkokin waje ta Rasha ta sanar da cewa za a bar jami'ai masu duba makamai masu guba daga hukumar hana amfani da makaman ta duniya su shiga birnin Douma a ranar Laraba.

Jami'an wadanda suke zaman jiran a ba su damar shiga domin gudanar da aikinsu tun ranar Asabar da suka hallara za su tattara abubuwan da za su iya gano samfurin makami mai gubar da aka yi amfani da shi a harin na Douma.

Kuma a ranar Talatar nan ne Syriar ke bikin ranar samun 'yancinta wadda ta kawo karshen mulkin Faransa a kanta a shekarar 1946.

Tunawa da wannan rana ta zo daidai da lokacin da manyan kasashen duniya uku, Amurka da Faransa da Birtaniya suka kai wa Syriar hari.

Shi ma Shugaba Assad na amfani da wannan lokaci ya nuna musu cewa yana nan da karfinsa, domin kusan kullum tun bayan harin na kasashen uku magoya bayansa sukan tattaru a tsakiyar Damascus su kewaye tutar kasar tasu suna tsine matakin na kasashen uku da cewa bai yi tasiri ba.

Labarai masu alaka