Yadda iyalan Shugaba Bashar al-Assad ke yawon shakatawa a Rasha

Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad da matarsa Asma a Damascus, a ranar 5 ga watan Satumba shekarar 2010 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Assad da matarsa Asma a birnin Damascus a 2010

Shugaban kasar Syria ya bayyana cewa a bara 'ya'yansa sun yi hutu a shahararen wurin yawon bude ido na matasa da ke Artek a Rasha .

Bashar al-Assad da matarsa Asma na da 'ya'ya maza biyu - Hafez me shekara 16 da Karim mai shekara 13 da kuma 'ya mace, Zein mai shekara 14.

Artek alama ce ta ta'addun kwaminisanci a lokacin tsohuwar Tarayyar Soviet, kuma har yanzu yana ci gaba da jan hankalin mutane.

Garin na kusa da yankin Kirimiya na kasar Ukraine wanda Rasha ta kwace a shekarar 2014.

Goyon bayan da sojojin Rasha suke nuna wa gwamnatin Assad, ya sake farfado da dangantaka mai karfi da ke tsakanin kasashen biyu a lokacin tsohuwar Tarayyar Soviet.

"Yarana sun je Artek a bara. Sakamakon baluguron da suka yi sun kara fahimtar Rasha yadda ya kamata," in ji shugaba Assad, a cewar dan Majalisar dokokin Rasha Dmitry Sablin, wanda suka gana da shi a birnin Damascus a ranar Lahadi.

Ganawar da suka yi da 'yan Majalisar dokokin Rasha ta biyo bayan harin makamai masu linzami da kasashen yamma suka kai wa kasar, yayin da kasashen yamman suka dora allhaki a kan sojoji Assad game da zargin harin makamai masu guba da aka kai.

Shugaban wurin yawon bude na Artek Alexei Kasprzhak, ya shaidawa sashen Rasha na BBC cewa bai san lokacin da yaran Assad suka zo wurin yawon bude ido na matasa ba.

"Yaran da ke zuwa wurinmu ba su cika ba mu sunnayen iyayensu ba," a cewarsa.

Image caption Artek alama ce ta ta'addun kwaminisanci a lokacin tsohuwar Tarayyar Soviet, kuma har yanzu yana ci gaba da jan hankalin mutane.

Sai dai sunan Assad ya ja hankalin mutane a wurin, in ji shi," kuma sai ya kasance cewa 'ya'yan Assad ne".

'Ya'yan Assad na cikin yaran Syria 44 da suka je hutu a Artek a bara, karkashin wani shiri da aka bullo da shi domin yaran sojojin Rasha.

Jiragen saman yaki na Rasha sun yi luguden wuta a wuraren da 'yan tawaye suke da iko a Syria, tun bayan da kasar ta shiga cikin yaki a watan Satumba na shekarar 2015, abin da ya bai wa sojojin gwamnatin Assad damar sake kwato wuraren da 'yan tawaye suka kwace.

Jakadan Syria a Moscow, Riad Haddad, a shekara dayar da ta gabata ya ce yaran Mr Assad na koyon harshen Rasha, kuma yanzu shi ne harshen kasashen waje da aka fi koyar wa a makarantun Syria.

Ya kuma ce iyaye da dama a Syria na bai wa 'ya'yansu maza suna "Putin" domin a girmama shugaban kasar Rasha.

Labarai masu alaka