Ana zargin R Kelly da sanya wa wata mata ciwon sanyi

R Kelly in 2015 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An zargi R Kelly da munanan dabi'u

Fitaccen mawakin nan na Amurka R Kelly na fuskantar sabuwar tuhuma kan zargin lalata, daga wata tsohuwar budurwarsa wadda ta yi zargin cewa ya sanya mata ciwon sanyi da gangan a birnin Dallas.

A cewar lauyanta, matar, wadda ba a fadi sunanta ba, ta shiga tsaka mai wuya a lokacin da suka yi mu'amala da mawakin ta tsawon wata 11.

An yi zargin cewa R Kelly mai shekara 51, ya yi kokarin sanya matar a wata kungiyar asiri ta wadanda ake yin lalata da su, wacce yake tafiyar da ita.

Hukumar 'yan sanda ta birnin Dallas ta ce tana bincike kan zargin.

A wata sanarwa da aka fitar gabanin taron manema labarai a ranar Laraba,lauyan matar Lee Merritt ya yi zargin cewa shekarar matar 19 a lokacin da suka fara mu'amalar lalata da Kelly.

Mr Merritt ya ci gaba da zargin mawakin da wasu munanan dabi'u da tursasa wa masu kananan shekaru shan barasa da mugayen kwayoyi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tun shekarun 1990 ake zargin mawakin da batun lalata

Kelly, wanda ya yi fice saboda wakokinsa da dama da suka hada da "I Believe I Can Fly," ya sha fuskantar tuhume-tuhume kan lalata, da yada hotunan batsa na yara da sauran laifuka makamantan haka.

A bara ne mawakin, wanda cikakken sunansa Robert Kelly, ya yi watsi da zarge-zargen cewa yana da kungiyar asiri da ke da 'yan mata da dama.

Jaridar The Washington Post ta ambato wani wakilin mawakin yana cewa "ya yi watsi da dukkan zarge-zargen."

Labarai masu alaka