An kama sanatan 'da ya sa aka sace' sandar majalisar dokokin Najeriya

senate Hakkin mallakar hoto Senate

Rundunar 'yan sandan Najeiya ta kama Sanata Ovie Omo-Agege, a harabar majalisar dokokin kasar, wanda ake zarginsa da tura 'yan daba don sace sandar majalisar dattawa.

Da safiyar ranar Larabar ne wasu da majalisar ta yi zargin 'yan daba ne karkashin jagorancin Sanata Omo-Agege, wanda aka dakatar da shi a makon da ya wuce, suka kutsa zauren majalisar yayin da ake zama, suka 'sace' sandar.

Sai dai har i zuwa yanzu Sanata Omo-Agege, bai ce komai ba game da zargin da majalisar ta yi masa na shiga da 'yan daba.

'Yan sandan sun kama shi inda suka sa shi a bakar mota suka yi gaba da shi.

Dama tun da fari majalisar ta bai wa Sufeto Janar na 'yan sanda da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS, umarnin su nemo sandar a cikin sa'a 24, sannan su kamo wadanda suka sace sandar.

Zuwa yanzu dai ba a san hukunci da jami'an 'yan sanda za su dauka a kan Sanata Omo-Agege ba.

Wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya fitar, ta bayyana wannan al'amari da cin amanar kasa, "don hakan tamkar kokari ne na kawar da wani reshe na gwamnatin tarayya da karfin tuwo, don haka dole a dauki duk matakin da ya dace.

Tuni dai an kawo wata sandar ta wucin-gadi an ajiye.

Sanata Sabi Aliyu ya kuma ce wannan abu ci fuska ne ga majalisar, kuma tuni shugabannin majalisar suka yi Allah-wadai da hakan.

'Yan majalisar dattawan sun yi wani taro na sirri inda suka tattauna lamarin, kafin daga bisani su dawo su ci gaba da zamansu kamar yadda suka tsara.

Mece ce Sandar Majalisa?

 • Sandar Majalisa da ake kira 'Mace' ta sha bamban da sauran alamun majalisar
 • Sandar tana da matukar muhimmancin gaske, inda majalisa ba za ta taba zama ba sai da ita
 • Sandar ita ce alamar iko a dukkan majalisun dokokin kasar na tarayya da na jihohi
 • Ana tafiya da Sandar a gaban shugaban majalisa a duk lokacin da zai shiga ko fita daga majalisar
 • Wani Sajan na Majalisar ne yake da alhakin daukarta a kafadarsa ta dama.

Wane ne Sanata Ovie Omo-Agege

Hakkin mallakar hoto Senate
Image caption Sanata Momo Agege
 • Sanata ne mai wakiltar Jihar Delta ta Tsakiya
 • Shekararsa 54
 • An dakatar da shi daga majalisar a makon da ya gabata saboda ya nuna adawa da sauya fasalin dokar zabe
 • Ya ci zabe karkashin jam'iyyar Labour LP
 • Ya taba aiki da hukumar 'yan sanda a shekarar 1987 zuwa 1988
 • Ya taba zama sakataren gwamnatin jihar Delta a 2007

Karin labaran da za ku so ku karanta:

Labarai masu alaka