Kun san sau nawa aka dauke sandar majalisa a Najeriya?

Sandar iko ta majalisar dattijai Hakkin mallakar hoto Nigerian Senate
Image caption Sandar iko ta majalisar dattijai

Da safiyar Laraba ne aka wayi gari wasu 'yan daba sun yi wa majalisar dattijan Najeriya dirar mikiya, inda ido na ganin ido suka dauke sandar majalisar suka yi gaba da ita.

An zargi Sanata Sanata Ovie Omo-Agege da jagorantar 'yan dabar da suka sace sandar zuwa majalisar.

Majalisar ta dakatar da Sanata Omo-Agege ne a makon da ya gabata saboda ya nuna adawa da sauya fasalin dokar zabe.

Yana wakiltar Jihar Delta ta Tsakiya daga jam'iyyar LP.

Hakkin mallakar hoto Senate
Image caption Sanata Momo Agege

Tuni dai rundunar 'yan sandan Najeriya ta kama sanatan bayan umarnin da majalisar ta bai wa hukumomin tsaro da a kamo wadanda suka sace sandar, sannan a dawo da ita cikin sa'o'i 24.

To amma ba wannan karon ne aka fara fara dauke sanda a majlisun kasar ba.

Mun yi waiwaye adon tafiya domin duba irin wasu lokutan da aka taba dauke sandar majalisa a Najeriya.

1965 Majalisar Wakilan Jihar Yamma

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An samu sabani tsakanin Obafemi Awolowo da Samuel Akintola abin da ya raba kan majalisar jihar yamma

Sace sandar majalisa a Najeriya ya samo asali ne tun a a jamhuriya ta farko, yayin da da wani rikici ya barke a majalisar dokokin Jihar Yamma 1965.

Rikicin ya samo asali ne daga sabani da rashin jituwa da suka kunno kai a jam'iyyar AG tsakanin shugaban jam'iyyar Chief Obafemi Awolowo da Firimiyan jihar yamma Chif Samuel Akintola.

Hayaniya ta barke a majalisar lokacin da aka yi zama domin tabbatar da tsige Akintola da gwamnan jihar ta yamma ya yi, inda Mista Ebubedike da ke wakiltar yankin Badagry ta Gabas ya dauke sandar majalisar yayin da rikici ya barke tsakanin wakilan majalisar.

Chuba Okadigbo 2000

Hakkin mallakar hoto The Sun Nigeria/Facebook
Image caption Chuba Okadigbo ya taba dauke sandar majalisar dattawa ya tafi da ita kauyensu.

Shekara 35 bayan rikicin majalisar dokokin jihar yamma, wani rikicin ya barke a majalisar dokokin Najeriya da ke Abuja.

Dangantaka ta yi tsami tsakanin shugaban Najeriya na lokacin Chif Olusegun Obasanjo da shugaban Majalisar Dattijai Chuba Okadigbo, lamarin da har ya kai an samu yamutsi a majalisar dattijan kasar a watan Afrilun 2000.

Rikicin ya barke ne bayan da wasu sanatoci da ake zargi suna goyon bayan shugaban kasa suka yi yunkurin tsige Chuba Okadigbo daga shugabancin majalisar.

Okadigbo ya dauke sandar majalisar zuwa gidansa, daga baya kuma ya tafi da ita kauyensu Ogbunike a jihar Anambara domin dakile tsige shi.

Majalisar Dokokin Jihar Rivers 2013

Hakkin mallakar hoto TVC/NEWS
Image caption Majalisar dokokin jihar Rivers

A matakin jihohi jihar Rivers ce ta kafa tarihi inda a watan Yuli na 2013 bayan wata hayaniyar ta kunno kai a majalisar dokokin jihar.

An fafata ne a lokacin tsakanin 'yan majalisa 27 da ke goyon bayan gwamnan jihar na lokacin Chibuike Rotimi Amaechi, da kuma wasu takwarorinsu biyar da ke goyon bayan karamin ministan ilimi na lokacin Nyesom Wike.

Su dai 'yan majalisar biyar sun ba da sanarwar tsige kakakin majalisar Otelemabama Amachree, sai dai mafi rinjaye daga ciki sun sun mayar da martani ta hanyar amfani da sandar majalisar wajen far wa 'yan majalisar biyar.

An ji wa uku daga cikinsu ciwo, inda har sai da aka garzaya da su asibiti.

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna 2013

Hakkin mallakar hoto Information Nigeria
Image caption An samu tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna da laifin dauke sandar majalisar

A ranar 24 ga watan Satumbar 2013 sandar majalisar dokokin jihar Kaduna ta yi batan-dabo.

An sace sandar ne yayin wata hatsaniya a majalisar da ta kai ga tsige shugaban majalisa na lokacin Alhaji Usman Gangara, da sauran shugabannin majalisar.

Wani kwamitin majalisar ya samu tsohon shugaban majalisar Alhaji Usman Gangara da laifin sace sandar, inda aka dakatar da shi daga majalisar tsawon wata uku.

A lokacin, an ci gaba da amfani da wata tsohuwar sanda ne a zaman majalisar, kafin a maido da wacce aka sace.

Majalisar Dokokin Anambara 2017

Hakkin mallakar hoto Newsinnigeria
Image caption Misis Rita Maduagwu ta dauke sandar majalisar dokokin jihar Anambara domin ta dakile yunkurin tsige ta.

A ranar 30 ga watan Mayun 2017, shugabar majalisar dokokin jihar Anambar Misis Rita Maduagwu ta yi gaba da sandar majalisar lokacin da wasu 'yan majalisa suka yi wani zama na yunkurin tsige ta.

Gabanin ta tsere da sandar, sai da gwamnan jihar Willie Obiano ya je majalisar domin shawo kan 'yan majalisar su dakatar da matakin, amma suka yi kunnen kashi.

Bayan duk wani yunkuri ya ci tura ne, shugabar ta yi awon gaba da sandar majalisar.

Sauran 'yan majalisar sun dau dogon lokaci suna jiran shigarta zauren majalisar, amma shiru.

Daga karshe dai an dage zaman majalisar saboda rashin sandar iko.

Mece ce Sandar Majalisa?

Sandar Majalisa da ake kira 'Mace' ta sha bamban da sauran alamun majalisar

Sandar tana da matukar muhimmancin gaske, inda majalisa ba za ta taba zama ba sai da ita

Sandar ita ce alamar iko a dukkan majalisun dokokin kasar na tarayya da na jihohi

Ana tafiya da Sandar a gaban shugaban majalisa a duk lokacin da zai shiga ko fita daga majalisar

Wani Sajan na Majalisar ne yake da alhakin daukarta a kafadarsa ta dama.

Hakkin mallakar hoto NIgerian senate

Labarai masu alaka