Sarauniyar Ingila Elizabeth za ta bude taron kasashen Commonwealth

Bana shekarar Sarauniya Elizabeth 92 a duniya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bana shekarar Sarauniya Elizabeth 92 a duniya

A ranar Alhamis ne Sarauniyar Ingila Elizabeth za ta bude taron shugabannin kasashen Commonwealth da zai gudana a fadar Buckingham.

A na sa ran shugabanni da Firai Ministocin kasashe Commonwealth 53 tare da iyalan gidan saurautar Burtaniya ne za su halarci taron.

Mai yiwuwa dai wannan shi ne taron shugabannin kasashen Commonwealth na karshe da Sauraniyar za ta bude da kanta.

Saboda a halin yanzu ba ta iya yin doguwar tafiya, kuma zai dauki dogon lokaci kafin shugabanni da Firai ministocin kasashen Commonwealth su sake taruwa a Landan.

A don haka taron zai kasance mai sosa rai kasancewar sarauniya ce ta rika lura da al'amuran kungiyar ta Commonwealth na tsawon shekaru-- a don haka kungiyar ke da matukar muhimmanci a gareta.

A baya dai wasu manyan kasashen Commonwealth kan tura mukarraban gwamnati ne don halartar taron da ake shirya wa.

Sai dai a wannan karon kusan daukacin shugabannin kasashen da Firai ministoci ne da kansu za su saurari jawabin sarauniyar a fadar.

Taken taron dai shi ne "domin cimma kyakkyawar makoma ta bai daya a nan gaba", ko da yake akwai batun makomar kungiyar ita kanta, saboda yadda lalitarta ke ci gaba da raguwa, kuma manufofinta ba a cika fito da su fili ba.

Masu lura da al'amura dai na ganin kafin kungiyar kasashen Commonwealth ta ci gaba da wanzuwa, wajibi ne a cika alkawuran da aka dauka a zahiri ba kawai a fatar baka ba a tsawon kwanaki biyu da shugabannin za su shafe suna wannan taron.