Matasan Najeriya sun fusata da kalaman Buhari

Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images

Matasa a Najeriya suna ta ce-ce-ku-ce tare da mayar da martani kan kalaman da Shugaba Buhari ya yi cewa mafi yawan matasa kasar ba ba suyi karatu ba kuma ba su da aikin yi, sannan suna jira gwamnati ta samar musu ababen more rayuwa da kudin mai.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a wajen taron kasuwanci na kungiyar kasashe rainon Ingila da aka yi a Westminster.

Ya ce Najeriya tana da yawan mutanen da suka haura miliyan 180, kuma kaso 60 cikin 100 na adadin wadannan mutane, matasa ne 'yan kasa da shekara 30.

Buhari ya ce, 'Da damansu ba su suyi makaranta ba, sannan suna cewa ai Najeriya kasa ce mai albarkar mai, don haka suna zaune ba sa komai suna jira gwamnati ta samar musu ilimi, da gida, da kula da lafiya kyauta'.

Matasan dai sun yi ta mayar da martani a kan wannan kalamai na shugaban kasar a kafofin sada zumunta, inda wasuunsu suka ringa yiwa shugaban ba'ar cewa ai matasan ne suka yi tsaiwar-daka har ya zama shugaban kasa.

Wannan batu dai na daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankalin matasan kasar, musamman ma da ya ke Shugaba Buhari ya fi farin jini a wajen matasa a sama da masu shekaru da yawa.

To sai dai duk da haka akwai wasu matasan da suke ganin babu aibu a maganar shugaban, domin kuwa bai hada matasan ya yi musu kudin goro ba, ya dai ce da dama daga cikinsu ne suka da wannan matsala.

Haka kuma wasu na da ra'ayin cewa gaskiya ce zalla shugaban ya fada, don haka babu wani abin tada jijiyar wuya.