An rantsar da Díaz-Canel a matsayin sabon shugaban Cuba

Miguel Díaz-Canel da Raúl Castro Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An dai rika tsamanin cewa Miguel Díaz-Canel shi ne zai gaji Raúl Castro

An rantsar da Miguel Díaz-Canel a matsayin shugaban kasar Cuba kuma zai maye gurbin Raúl Castro wanda ya karbi mulki daga hannun dan uwansa mai fama da rashin lafiya Fidel a 2006.

Wannan ne karon farko da ake samun wani wanda ba dangin Castro bane a matsayin shugaban kasa tun bayan juyin juya halin da aka yi a shekarar 1959 .

Mr Díaz-Canel shi ne mataimakin shugaban kasa shekaru biyar da suka gabata.

Duk da cewa bayan juyin-juya-hali ne aka haifi Mr Díaz-Canel, yana da kusanci sosai da Raúl Castro kuma ana kyautata zaton cewa ba zai aiwatar da wani gagarumin sauyi ba.

Gaba dayan 'yan majalisar dokokin kasar 605 da aka zaba a watan Maris ne suka zabe shi, bayan da ya tsaya takara shi kadai ba hamayya.

Ana dai sa ran cewa Mista Castro zai cigaba da yin tasiri a harkokin siyasar kasar a matsayinsa na jagoran jami'yyar kwaminisanci ta Cuba.

A jawabin da ya gabatar, Mr Díaz-Canel ya ce manufarsa ita ce ya ci gaba da daukar ranar juyin-juya-halin Cuba a matsayin rana mai tarihi, kuma ya tabbatar wa yan majalisr dokoki da cewa " za a ci gaba da bin turbar juyin-juya-halin".

Ya ce ba zai sauya manufofin kasar kan harkokin kasashen waje ba, kuma duk wani sauyin da za a yi game da haka, toh 'yan Cuba ne za su dauki wannan mataki.

Mista Diaza-Canel ya kuma ce gwamnatinsa ba za ta rungumi masu fafitukar sake dawo da tsarin jari hujja ba.

A cikin jawabin na sa ya yabawa Raúl Castro da ya gaji mulki daga wurinsa inda ya ce "Cuba na bukatarka". Wannna ya sa mambobin 'yan majalisar su 600 suka tashi tsaye suna tafi domin karama mutumin mai shekara 86.

Sai dai duk wani sauyin da Mista Díaz-Canel zai kawo, za a yi shi ne a hankali kuma tare da yin la'akari da sauye-sauyen da Raúl Castro ya kawo tun bayan da ya karbi mulki daga hannun'yayansa Fidel.

Dole ne sabon shugaban kasar ya yi nazari a kan yadda zai shawo kan matsalolin da durkushewar tattalin arziki ta haifar a Venezeula wacce abokiyar Cuba ce da kuma irin dangantakar da kasarsa za ta yi da Amurka karskashin shugabancin Donald Trump.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Cuba zasu so su ga yadda sabon shugaban kasar zai inganta rayuwarsu

A bara ne dai sabon shugaban kasar Amurkan ya sake aiwatar da dokar hana tafiya da kuma kasuwanci wanda gwamnatin Barack Obya ta yiwa sassauci, sai dai be dakatar da yin huldar diplamasiya tsakninsu ba.

'Yan Cuba da dama za su zuba ido su ga kamun ludayin sabon shugaban kasarsu a kan yadda zai inganta rayuwarsu.

Labarai masu alaka