Shugaban Afirka Ta Kudu ya katse taron Commonwealth saboda zanga-zanga

Mr Ramaphosa wanda ya karbi mulki a watan Fabrairu ya yi alkawarin kawo canji a kasar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Ramaphosa wanda ya karbi mulki a watan Fabrairu ya yi alkawarin kawo canji a kasar

Shugaban Afirka Ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya katse taron kasashen Commonwealth da yake halarta a Burtaniya domin shawo kan rikice-rikice da ke gudana a kasarsa.

Shugaban kasar wanda ya karbi ragamar mulki hannun Jacob Zuma, ya yi amfani da halartar taron ne don jawo hankalin masu zuba jari zuwa Afirka ta Kudu.

Mr Ramaphosa wanda ya karbi mulkin Afrika ta Kudun a watan Fabrairu ya yi alkawarin kawo sauyi a kasar.

Sai dai mai yiwuwa zai ji takaicin yadda ala tilas ya bar taron Commonwelath na farko da yake halarta don ya fuskanci halin da ake ciki a kasarsa.

Tun a ranar Laraba ne dai rikici ya fara barkewa a lardin arewa maso yammacin kasar.

Masu zanga-zanga na kokawa ne kan rashin ayyukan yi da gidaje tare da neman a kawo karshen aikata cin hanci da kuma sallamar Firimiyar ANC a lardin.

An kuma rufe hanyoyi inda wasu bata-gari suka rika kona motoci da kwasar ganima a shaguna.

Mr Ramaphosa ya yi kira da a kwantar da hankula inda ya umurci 'yan sanda da su yi taka-tsan-tsan a kokarin da suke yi na shawo kan zanga-zangar.

Labarai masu alaka