Labaran Afirka na mako guda cikin hotuna

Zababbun hotuna mafi kyau daga Afirka da na mutanen Afirka a wasu wurare a duniya na wannan makon.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mutane a bikin Popo a kudu maso gabashin Ivory Coast suna sanye da kayan ado a ranar Asabar..
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hoton "Togo street" a Berlin ranar Asabar bayan Yan siyasa sun amince da canza sunan hanyoyi da suka hada da musiban da Jamus suka haddassa a yayin da suke mulkin mallakan Afrika.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Ivory Coast a rana karshe ta bikin Popo a Bonoua, a ranar 14 ga watan Afrilu 2018. a lokacin bikin na Popo and wasanni masu gamsarwa, da gasar mata ta tafi kowa kyau, da raye-raye na gargajiya, da kuma ziyartar gidajen tarihi na Popo.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption wasu kuma sun yi amfani da fanti a fuska dan kwalliyya..
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Eliud Kipchoge, daya daga cikin masu tseren gudun famfalaki na London, ya dauki hoto gabanin tseren 2018 na ranar alhamis.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ranar Litinin, wani rukunin yan matan Somalia suna magana gami da dariya tare a sansani yan' gudun hijirar Dadaab a Kenya .
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Laraba ne wasu 'yan daba suka sace sandar iko daga Majalisar Dattijan Nijeriya. An gano sandar washe gari a karkashin wata gada a babban birnin tarayya, Abuja
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Marubuciya 'yar Najeriya Chimamanda Ngozi Adichie tana jawabi a wajen taro kan zazzabin cizon sauro a birnin London ranar 18 ga watan Aprilu, 2018. An gudanar da taron ne domin jan hankalin shugabannin kasashe rainon Ingila su kara kaimi wajen magance cutar a kafatanin kasashe kungiyar Commonwealth cikin shekaru biyar masu zuwa.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban mutane su halarci jana'izar Winnie Madizikela-Mandela ranar Asabar.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An gudanar da jana'izar ne a Soweto kusa da inda mai fafutukar yaki da wariyar launin fata ta zauna.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sai da kasa ta motsa a filin na Orlando yayin da dubban mutane suka raira wakokin 'yanci, sannan suka gode wa gudummawar da Winnie Mandela ta bada, wadda suke kira Mama Winnie.
Hakkin mallakar hoto AFP
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Naomi Campbell ta ziyarci jana'izar tare da iyalin Mandela..
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A Zimbabwe, yara sun zauna inda suka fitar da hoton Shugaban kasa Emmerson Mnangagwa a lokacin murnar bikin ranar samun 'yanci ranar Laraba.

Hotuna daga AFP, da Getty Images da kuma EPA

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC