Kotu za ta yanke wa maharin Paris hukunci

Salah Abdeslam Hakkin mallakar hoto BELGIAN/FRENCH POLICE
Image caption A watan Maris na 2016 aka kama Abdeslam bayan musayar wuta da 'yan sanda a Brussels

Wata kotu a birnin Paris za ta yanke wa mutum daya da ya tsira da rai daga cikin wadanda suka kai harin birnin Paris na 2015 wanda ya hallaka mutane 130, a wata tuhumar ta kokarin halaka 'yan sandan Belgium.

Mutumin da ya taba kasancewa wanda aka fi nema ruwa a jallo a nahiyar Turai Salah Abdeslam mai shekara 28, ya kasance a gidan wakafi tsawon shekara biyu, kuma zargin da ake masa na hannu a harin da aka kai Paris a shekara ta 2015, wanda ya hallaka mutane 130, ba a gabatar da shi a gaban wata kotu ba zuwa yanzu.

To amma a ranar Litinin din nan wata kotu, za ta yanke hukunci a wata tuhumar ta daban da ta hada da Abdeslam da kuma wani mutumin na biyu da ake zargi mai suna, Soufiane Ayari, inda ake zarginsu da laifin yunkurin kashe jami'an 'yan sandan Belgium, yayin da 'yan sandan suke kokarin kama Abdeslam a wani wuri da ya boye a wani gari da ke wajen birnin Brussels.

An ji wa jami'an tsaron uku rauni a yayin wannan tataburza, a lokacin da aka bude musu wuta, wanda kuma a wannan lokaci su kuma suka yi nasarar kashe mutum daya daga cikin wadanda ake zargi da ta'addancin,

Kafin kuma su kai ga kama Abdeslam wanda ya yi kokarin tserewa ta kan rufin dakuna.

Yana dai fuskantar hukuncin daurin shekara 20 a gidan jarun, idan aka same shi da laifi.

Amma dai yanzu yana tsare a wani kebabben wuri, na kare-kukanka, a kusa da birnin Paris, kuma ana ganin ya ki yarda ya halarci zaman kotun na Litinin, wanda a lokacin za a yanke masa hukunci.

Labarai masu alaka