Kotu ta yanke wa maharin Paris hukuncin daurin shekara 20

Salah Abdeslam Hakkin mallakar hoto BELGIAN/FRENCH POLICE
Image caption A watan Maris na 2016 aka kama Abdeslam bayan musayar wuta da 'yan sanda a Brussels

Kotu a Belguim ta yanke wa Salah Abdelsalam, mutumin da ya tsira a cikin maharan da suka kai hari a birnin Paris, hukuncin daurin shekara 20 a gidan kaso saboda samnsa da laifin musayar wuta da suka yi da jami'an tsaro lokacin da aka je kama shi.

Kotun ta kuma sami Abdeslam mai shekarar 28 da kuma Sofien Ayari da laifi game da tuhumar da ake yi mu su ta yunkurin kisa.

An yanke wa Ayari, mai shekara 24 hukuncin daurin shekara 20 a gidan kaso.

Dukannin mutunensu biyu sun bude wa jami'an 'yan sanda wuta lokacin da suka kai sumame a wani gida da ke Brussels a shekarar 2016.

Ana dai tsare da shi a Faransa kuma nan bada jimawa ba zai bayyana a gaban wata kotu da ke Faransa dangane da hare-haren da aka kai a birnin Paris.

Salah ya ki ya amsa tambayoyin da alkaliyar kotun ta rika yi masa a shari'ar da aka yi a Brussels kuma daga bisani yaki zuwa zaman kotun.

Salah da Ayari ba su halarci zaman kotu ba a lokacin da aka yanke mu su hukuncin ranar Litinin.

Kotu ta yanke wa kowanensu hukuncin daurin shekara 20 kamar yadda mu su gabatar da kara suka bukata.

Mai shari'a Marie France Keutgen, ta ce ba bu "tantanma" mutanen biyu na mu'ammala da masu "tsananin" kishin Islama.

A ranar 15 ga watan Maris na shekarar 2016, 'yan sandan Belguim da ke farautar Abdeslam suka kai sumame a wani daji da ke Brussels.

Sun kai sumame a wani gida da sukayi ammanar cewa Salah na smun mafaka wanda aka yi watanni ana nemansa ruwa a jallo.

Labarai masu alaka