'Jami'an tsaro sun yi wa gidan Sanata Dino Melaye dirar mikiya'

Sanata Dino Melaye Hakkin mallakar hoto Facebook Dino Melaye
Image caption Sanata Dino Melaye ya ce an kama shi ne da safiyar Litinin

Jami'an tsaron Najeriya sun mamaye gidan Sanata Dino Melaye da ke unguwar Maitama a Abuja, bayan sun kama shi a filin jirgin sama.

Sanatan ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa 'yan sandan kwantar da tarzoma fiye da "30 dauke da manyan makamai" ne suka yi wa gidansa kawanya a ranar Litnin.

Sai dai har yanzu jami'an tsaron kasar ba su ce komai ba dangane da batun.

BBC ta yi kokarin ji ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan kasar Jimoh Moshood, amma ya ki daukar wayarsa kuma bai ba da amsa kan sakon wayar da aka aike masa ba.

"A yanzu haka sun rufe hanyar gidana ba shiga, ba fita," a cewar Sanata Dino.

Tun da farko hukumomi a Najeriya sun kama 'dan majaisar dattawan kasar Sanata Dino Melaye a safiyar Litinin.

Mr Melaye ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa an kama shi ne a filin jirgin sama na Abuja.

Sai dai wasu bayanai da BBC ba ta tabbatar ba suna cewa an sallami sanatan.

Sanatan ya kara da cewa "an kama shi ne bayan ya wuce shingayen bincike na jami'an tsaro domin tafiyar aiki zuwa kasar Morocco".

Kawo yanzu babu bayani daga hukumomin tsaro kan batun kama Sanata Melaye.

Tuni da ma 'Yan sandan kasar suka bayyana Sanatan, mai wakiltar Kogi ta Yamma a matsayin wanda suke nema ruwa-a-jallo.

'Yan sandan na zarginsa da kin bayyana a gaban kotu domin fuskantar shari'a kan zargin daukar nauyin wasu mutane su tayar da hankali da aikata miyagun laifuka.

Sai dai sanatan ya yi watsi da dukkan zarge-zargen yana mai cewa siyasa ce kawai.

Sanata Dino Melaye, wanda na hannun damar Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ne, yana jawo ke-ce-kuce saboda kalamansa na siyasa da kuma salonsa na son rayuwar kasaita.

Mr Melaye ya ce an kama shi ne a kan hanyar tafiyar da gwamnatin Najeriya ta dauki nauyi.

"An hana ni tafiya, amma kuma ba gudu ba ja da baya, ba za mu daina magana ba," kamar yadda wallafa a shafinsa na Twitter.

Hakkin mallakar hoto Dino Facebook

Dino Melaye a takaice

  • Dan asalin jihar Kogi, amma an haife shi a Kano
  • Shekararsa 44
  • Ya yi karatun firamare a Kano
  • Ya yi digirinsa a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria
  • Yana wakiltar Kogi Ta Yamma a majalisar dattawa
  • Ya taba zama dan majalisar waklilan Najeriya har sau biyu
  • An san shi a tarar aradu da ka a harkokin siyasa
  • Ya taba karbar lamar yabo na dan majalisar wakilan da babu kamarsa daga wata kungiyar matasa

Karin labaran da za ku so ku karanta:

Labarai masu alaka