Ba ni da matsala da Mourinho – Pogba

A shekarar 2016 ne Pogba ya koma Machester United da ga kungiyar Juventus kan fam miliyan 89 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A shekarar 2016 ne Pogba ya koma Machester United daga kungiyar Juventus kan fam miliyan 89

Dan wasan Manchester United Paul Pogba ya ce ba shi da matsala da Jose Mourinho, kuma baya tunanin barin kungiyar a karshen kakar bana.

Dan wasan tawagar Faransa mai shekara 25, bai buga karawar da Sevilla ta fitar da United a gasar Champions League da suka kara a watan fabarairu da Maris ba.

A watan Augusta shekarar 2016 Pogba ya koma United a kan fam miliyan £89, inda ya kafa tarihi kuma ya taimaka wa kungiyar wajan daukar kofin gasar zakarun turai ta Europa a kakar bara.

Ya kasance cikin 'yan wasan da suka rika taka-leda akai-akai, amma akasin haka ake gani a watannin baya bayanan , inda kocin tawagar kwallon kafa ta Faransa Didier Deschamps ya ce dan wasan tsakiyar "baya jin dadi" kan halin da yake ciki.

A watan fabarairu ne Mourinho ya bayyanna rahotanni da ke cewa Pogba ya yi nadama komawa United a matsayin maganar da ba ta da tushe.

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola a watan da muke ciki ya ce an yi masa tayin sayan dan wasan a watan Janairu.

Pogba y ce : "Mourinho ne ya sa na zama kyaftin. Shi ne ya bani wannan dama a kugiya mai mahimmaci irin Manchester United."

" Ya zuwa yanzu ina Manchester United kuma ina magana ne a kan abubuwan da ke faruwa yanzu. Mun kai wasan karshe a gasar cin kofin FA, kuma zan je gasar cin kofin duniya.

Labarai masu alaka