An kashe Mutum 10 da Mota a Toronto

'Yan sanda tsye a wurin motar da aka yi amfani da ita a harin Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sanda sun killace motar da aka yi amfani da ita wajen kai harin

Mutum goma sun mutu yayin da wasu akalla 15 suka samu raunuka a lokacin da wani direban mota ya yi kan masu tafiya a kafa a gefen titi a birnin Toronto na Canada.

Jami'an tsaro da ke rike da direban motar yanzu sun ce da gangan ya aikata abin.

Rahotanni sun ce da rana ne abin ya faru, inda kwatsam ba zato ba tsammani aka ga wata farar mota ta bar titi kawai ta hari gefen da mutane ke tafiya da kafa, a wata mahada da ke da hada-hadar jama'a da ababen hawa, a wata unguwa da ke arewacin birnin Toronto.

Wadanda suka ga yadda lamarin ya faru, sun ce a lokacin ba abin da ake ji sai ihun jama'a, yayin da motar ke bi ta cikinsu har kusan tsawon rabin mil daya kafin daga bisani ta dawo kan titi.

''Direban ya kara komawa da motar inda masu tafiya da kafa ke bi, haka dai ya yi ta yi yana tattake mutane.''

Magajin garin na Toronto John Tory ya roki jama'a da su kwantar da hankalinsu, a yayin wani jawabi da ya yi ga manema labarai jim kadan da faruwar abin.

Hukumomi dai sun ce hari ne da aka kai da gangan, yayin da 'yan sanda suka bukaci mutanen da suka ga yadda abin ya faru su je domin bayar da shaida.

Abin ya faru ne a wurin da ke da nisan mil 18 daga birnin na Toronto, inda ministocin manyan kasashe bakwai masu arzikin masana'antu ke taro.

Kawo yanzu dai ba a san dalilin kai harin ba, wanda ya yi kama da irin wanda 'yan kungiyar IS masu ikirarin jihadi ke kaiwa a wasu kasashen.