An kwantar da tsohon shugaban Amurka George H.W. Bush a asibiti

George H.W. Bush ( a hagu) da Barbara da Bush karami Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kwantar da George H.W. Bush ( a hagu) a asibiti ne kwanaki bayan mutuwar matarsa Barbara (a tsakiya)

An kwantar da tsohon shugaban Amurka, George H.W. Bush, a wani sashe da ake kula da masu cutar da ta yi tsanani a wani asibiti da ke Texas, 'yan kwananki bayan mutuwar matarsa, Barbara.

Madam Bush mai shekara 92, ita da mijinta sun yi aure tsawon shekara 73, wanda wannan shi ne aure mafi tsawo ko dadewa na wani shugaban Amurka a tarihi.

An binne Barbara Bush ne ranar Asabar, inda mijin nata da tsoffin shugabannin Amurkar Bill Clinton da Barack Obama da George W. Bush da matansu, hadi kuma da matar shugaban na yanzu Melania Trump suka halarta.

A wata sanarwa da mai magana a madadin iyalan tsohon shugaban, Jim McGrath ya fitar, ya ce tun ranar Lahadi aka kwantar da Bush Babba, mai shekara 93, bayan kamuwa da wata cuta da ta yadu a jininsa.

Sai dai kakakin na iyalan na Bush ya ce yana samun sauki.

Shekara daya da ta wuce a daidai wannan watan Mista Bush ya shafe mako biyu a asibiti domin jinyar cutar sanyin hakarkari da kuma ta wata mai tsanani ta huhu.

A yanzu dai George Bush shi ne tsohon shugaban kasar Amurka mafi dadewa da ke a raye, kuma y yi shugabancin ne tsakanin 1989 da 1993.