Hisba ta tsince yara fiye da 26,000 a titunan Kano – Sheikh Daurawa

Sheikh Aminu Daurawa
Image caption Malamin ya ce bai ga dalilin haihuwar 'ya'yan da ba za iya rike su ba

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta ce a shekara biyun da ta wuce ta tsinci yara fiye da 26,000 da ke gararamba a titunan jihar.

A cewar hukumar, galibin yaran da aka tsinta dai sun fito ne daga wasu kasashe masu makwabtaka da Najeriya da kuma jihohin kasar masu makwabtaka da jihar Kano.

Shugaban hukumar, Sheikh Aminu Daurawa, ya ce bai ga dalilin haihuwar 'ya'yan da ba za ka iya rike su ba.

Hakazalika malamin ya ce babu wani dalili da zai ya sa ka bar yaro kankani yana gararamba a kan titi. Ya ce laifi ne babban ka haifi mutum kuma ka jefar da shi a kan titi.Ya ce idan sun tsinci yaro ba su ne suke kula da su ba.

Ya ce suna mayar wa iyayen yaran ne kuma su ja musu kunne kan su mayar da hankali tarbiyyarsa.

"Wadanda kuma ba a samu iyayensu ba, suna ba mu wahala. Wani babu garinsu, babu cikakken bayani da zai fada maka daga ina yake."

Ya ce idan suka samu irin haka suna kai wa kwamiti da gwamnati ta kafa don kula da irin wannan hali.

  • Latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirar
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hirar BBC da Sheikh Daurawa

Labarai masu alaka