'Yan sanda sun sake cafke Dino Melaye bayan ya 'tsere' tun da farko

Dino Hakkin mallakar hoto Facebook
Image caption Dino Melaye ya musanta zargin da 'yan sandan ke masa

'Yan sanda sun sake cafke Sanata Dino Melaye bayan da tun da farko wadansu mutane da ake kyautata zaton magoya bayan sa ne suka taimaka ya tsere a Abuja.

Rahotanni sun ce 'yan sandan sun sake kame Sanatan ne bayan an kwantar da shi a asibitin Zankli da ke birnin Abuja.

Shi dai Sanata Dino Melaye ya kufce ne daga hannun jami'an 'yan sanda a lokacin da suke kan hanyar tafiya da shi zuwa Lakoja, babban birnin jihar Kogi.

Wani jami'in 'yan sandan ya shaida wa BBC cewa Mr Melaye ya tsere wa kamun da aka yi masa tare da taimakon wasu magoya bayansa.

Wakiliyar BBC Dooshima Abu wacce ta ziyarci asibitin a lokacin da yake kwance ta ce motocin 'yan sanda da dama sun killace asibitin kafin daga bisani suka sake kama shi.

Tun da farko a ranar Talata Sanatan ya mika kansa ga 'yan sanda bayan da suka yi wa gidansa kawanya.

Bayanai sun nuna cewa ana shirin kai sanatan ne zuwa mahaifarsa ta Kogi domin a gabatar da shi tare da wasu da ake zargi da aikata miyagun laifuka.

Sai dai kwamishinan 'yan sandan jihar ta kogi, Ali Janga, ya shaida wa Premium Times cewa ba shi da niyyar gabatar da sanatan ga jama'a, sai dai kawai ya shirya yin taron manema labarai ne kan batun.

Tuni da ma 'yan sandan kasar suka bayyana shi a matsayin wanda suke nema ruwa-a-jallo.

'Yan sandan na zarginsa da kin bayyana a gaban kotu domin fuskantar shari'a kan zargin daukar nauyin wasu mutane su tayar da hankali da aikata miyagun laifuka.

Sai dai sanatan ya yi watsi da dukkan zarge-zargen yana mai cewa siyasa ce kawai.

Sanata Dino Melaye, wanda na hannun damar Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ne, yana jawo ke-ce-kuce saboda kalamansa na siyasa da kuma salonsa na son rayuwar kasaita.

Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Dino Melaye lokacin da ya fado daga motar 'yan sanda
Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Dino Melaye lokacin da ya isa asibiti
Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Dino Melaye ana shiga da shi asibiti

Dino Melaye a takaice

Hakkin mallakar hoto Dino Facebook
  • Dan asalin jihar Kogi, amma an haife shi a Kano
  • Shekararsa 44
  • Ya yi karatun firamare a Kano
  • Ya yi digirinsa a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria
  • Yana wakiltar Kogi Ta Yamma a majalisar dattawa
  • Ya taba zama dan majalisar waklilan Najeriya har sau biyu
  • An san shi a tarar aradu da ka a harkokin siyasa
  • Ya taba karbar lamar yabo na dan majalisar wakilan da babu kamarsa daga wata kungiyar matasa

Karin labaran da za ku so ku karanta:

Labarai masu alaka