Dalibai 13 sun mutu bayan motarsu ta yi karo da jirgi

Motar tayi hadari ne yayin da tsallaka hanyar jirgin da babu mai bada hannu
Image caption Motar ta yi hadari ne yayin da ta tsallaka hanyar jirgin da babu mai bada hannu

Yara 'yan makaranta 13 ne suka mutu yayin da motarsu ta yi karo da jirgin kasa a jihar Uttar Pradesh ta Indiya., kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.

Motar na tafiya ne a kan wani layin dogo da babu jami'an kula da hanya lokacin da hadarin ya faru.

Wannan lamari ya faru ne 'yan makonnin kadan bayan yara 24 sun mutu yayin da motarsu ta fada a cikin wani kwazazzabe a jihar Himachal Pradesh.

Hadarin mota na afkuwa akai-akai a Indiya, sau da yawa saboda rashin iya tuki ko kuma hanyoyi da motoci marasa kyau.

Wannan hadarin ya faru ne a yankin Kushinagar na jihar Uttar Pradesh.

Har yanzu ba'a san yara nawa ne ke tafiya a cikin motar ba.

Gwamnatin jihar ta umarci a gudanar da bincike game da wannan lamari kuma ta sanar da biyan diyya ga iyalan wadanda aka kashe a hadarin.

Wata sanarwa daga Babban Ministan Yogi Adityanath ya ce yana kan hanyarsa ta zuwa inda lamarin ya faru.

Labarai masu alaka