Me ya sa Akshay Kumar zai yi gwanjon tufafinsa?

Akshay Kumar sanye da kakinsa a fim din Rustom Hakkin mallakar hoto E TIMES
Image caption Akshay Kumar sanye da kakinsa a fim din Rustom

Jarumi Akshay Kumar na gwanjon kakin da ya saka a fim din Rustom domin amfani da kudin wajen tabbatar da kariya da kuma walwalar dabbobin kasar Indiya.

Ana yi wa jarumin kallon mutumin da yake da kyakkyawar zuciya da tausayi.

Sau da yawa jarumin ya kan bayar da taimako a kan wasu batutuwa da suka shafi kasar Indiya.

A yanzu ma ya sake yunkuri domin taimakawa wani shiri na tabbatar da cetowa da kuma walwalar dabbobi.

A wannan lokaci ya yi amfani da wata sabuwar dabara don jawo hankalin mutane a kan wannan batu.

A wannan karon Akshay ya fito da kakin da ya saka a film din Rustom domin gwanjonsa.

Akshay kuma ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "Ina mai farin cikin sanar da ku cewa wani daga cikinku zai iya cin gasar gwanjon kakin da na saka a fim din Rustom."

Za a kawo karshen gwanjon ne a ranar 26 ga watan Mayun bana.

Takaitaccen labarin fim din Rustom

Akshay Kumar wanda ya kasance jarumi a fim din na Rustom, ya taka muhimmiyar rawa inda ya fito a matsayin babban sojan ruwa wanda ake matukar ganin kimarsa saboda amana da iya aiki.

Hakan ya sa ake yawan tura shi aiki zuwa wurare daban-daban kuma ya kan shafe watanni idan ya yi tafiya.

Saboda yawan tafiye-tafiyensa ya sa matarsa Ileana D'Cruz, ta kasa jure kadaicin da ke damunta, sai ta fara soyayya da abokin mijinta, har ta kai Akshay Kumar din ya kama su tare bayan ya yi dawowar ba-zata gida.

Haka ya sanya shi dogon bincike ya kuma gano cewa matarsa na mu'amala da abokinsa idan baya nan.

Sai ya tunkare shi a gidansa kuma a cikin dakinsa suna kokawa, sai abokin nasa ya fito da bindiga zai harbe shi.

Daga nan, shi kuma ya kare kansa ta hanyar harbin abokinsa na sa, nan take kuma ya ce ga garinku nan.

Wannan dalili ya sa aka kai shi a kotu aka yi shari'a, har daga karshe aka gano cewa Akshay ba shi da laifi aka wanke shi.

Hakkin mallakar hoto E TIMES
Image caption Akshay Kumar tare da sauran jaruman da suka fito a fim din Rustom

Tinu Suresh Desai shi ne ya bayar da umarnin fim din Rustom, yayin da Neeraj Pandey kuma ya shirya shi.

A watan Agustan shekarar 2016 aka saki fim din Rustom, kuma yana daga cikin fina-finan da suka yi tashe a shekarar.

Akshay Kumar ya karbi lambobin yabo da dama albarkacin fim din Rustom.

Labarai masu alaka