Mene ne dalilin hana Atiku shiga Amurka?

Mene ne dalilin hana Atiku shiga Amurka?
  • An sabunta wannan labari bayan da aka fara wallafi shi a watan Afrilun 2018.

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya ce ya nemi izinin shiga Amurka, amma an hana shi.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da Jimeh Saleh bayan wata ziyara da ya kai ofishin BBC da ke Landan a watan Afrilun bana - wato kafin tsayar da shi a matsayin dan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP a zaben 2019.

Ya musanta cewa an yi gwanjon wani gidansa na Amurka, inda ya ce gidan matarsa ne, kuma "ita ta sayar da gidanta ta karbi kudinta."