Ba ma so a kara shiga rigar Buhari - 'Yan Majalisa
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ba ma so a kara shiga rigar Buhari - 'Yan Majalisa

Wasu 'yan Majalisar wakilan Najeriya sun bayyana dalilansu na yin kwaskwarima a dokokin zabe, wanda kotu a kasar ta ce ba su da hurumi.

'Yan Majalisar Dokokin suna son a sauya yadda ake gudanar da zabe inda na shugaban kasa zai zo a karshe. To sai dai bangaren zartarwa na adawa da wannan mataki na majalisar.

To amma daya daga masu rajin yin gyara a dokokin zaben Hon. Muhammad Musa Soba ya ce sun dauki matakin ne da kyakkyawar manufa.