Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka a makon jiya

Wasu daga cikin hotuna masu kayatarwa na Afirka na wannan mako.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wata agwagwar ruwa da ake kira Penguin a bakin teku a birnin Cape Town da ke kasar Afirka ta Kudu
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wani mutum ya tsaya a gaban wata mota a bikin raya al'adun gargjiya na bana a garin Tankwa Karoo da ke Calvinia a kasar Afirka ta Kudu, a ranar 24 g watan Afrilun ta 2018
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mutum 13,000 ne suka halarci bikin na bana ciki har da wannan mutumin da ya sanya abin rufe fuska da aka yi da kasusuwa
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Biki ne da ake yi wa fuska ado sosai kamar yadda wadannan mutanen suka yi
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ma'aikata a Afrika ta Kudu yayin wata zanga-zangar neman karin albashi a garin Cape Town a ranar 25 ga watan Afrilu
Hakkin mallakar hoto Taiwan presidential office
Image caption Wadansu 'yan wasan kwaikwaiyo da ke sanye da tufafi mai launin tutar kasar Swaziland na rawa a bikin cikar kasar shekara 50 da samun 'yancin kai da kuma cikar Sarki Mswati na uku shekara 50 da haihuwa
Hakkin mallakar hoto Taiwan presidential office
Image caption Wadannan matan na cikin wadanda suka halarci bikin
Hakkin mallakar hoto Taiwan presidential office
Image caption Sarki Mswati na uku na yanka kek, yayin da shugabar kasar Taiwan Tsai Ing-wen, na cikin manyan bakin da aka gayyata
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wadansu mata a Uganda sun ajiye furenni a wurin tunawa da wadanda aka kashe a kisan kiyashin da aka yi a Rwanda shekara 24 da ta gabata
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An gano dala a wurin binciken kufai da ke Bajarawiya, a Sudan...
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An gano wadansu kayayyakin kufai a wurin da kabarin Sarki Khalmani yake a cikin dalar. Ya yi mulki a masauratar Meroitic tsakanin shekarar 186 zuwa 207 kafin zuwan Annabi Isa (AS)
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wadansu yara sun zana jakin dawa akan bango a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, domin wayar da kan jama'a kan muhimmancin kare hakkin bil'adama da kuma na dabobi a ranar Laraba
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani makeri na shan shisha a cikin shagonsa a garin Iskandriya na kasar Masar ranar Litinin
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A garin Grombalia na Tunisia wannan matar na gasa burodi a wurin gasa burodi na gargajiya da aka yi da laka
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata mawakiya 'yar kasar Kwaddibuwa "Valerie" a bikin kade-kade da raye-raye da aka yi a birnin Abidjan ranar Lahadi

Hotuna daga AFP, Getty Images, Reuters da kuma EPA

Labarai masu alaka

Labaran BBC