Sabbin jaruman da ka iya mamaye fina-finan Indiya a 2018

1. Janhvi Kapoor

Hakkin mallakar hoto The Express Tribune

Janhvi ita ce babbar 'yar marigayiya Sridevi, kuma 'ya a wajen mai shirya fim Boney Kapoor.

Janhvi za ta fara fim ne da kamfanin Dharma Production, wato kamfanin Karan Johar.

Dhadak, shi ne fim din da za a fara ganin Janhvi a ciki, wanda za su fito tare da Ishaan Kapoor.

Dhadak fim ne na soyayya, wanda ya kunshi soyayya tsakanin 'yar masu hannu da shuni da kuma dan talaka.

Shashank Khaitan, shi ne wanda ya bayar da umarnin fim din, kuma Karan Johar na daga cikin mutum uku da suka shirya shi.

Za a saki fim din Dhadak a ranar 20 ga watan Yulin 2018. Shekarun Janhvi a yanzu 22.

2. Ishaan Khattar

Hakkin mallakar hoto The Express Tribune

Ishaan kani ne a wajen jarumi Shahid Kapoor.

Mahaifiyarsu daya, amma uba daban-daban.

A 2018, Ishaan ya yi fina-finai biyu, wato Beyond the Clouds, wanda fim ne na darakta Majid Majid dan kasar Iran, sai kuma Dhadak wanda shi ne fim dinsa na Indiya na farko da zai fito.

Dhadak fim ne wanda za su fito tare da Janhvi Kapoor.

Shekarun Ishaan a 2018, 22, amma zai cika 23 a watan Nuwamba.

3. Sara Ali Khan

Hakkin mallakar hoto The Express Tribune

Sara ita ce babbar 'ya a wajen jarumi Saif Ali Khan da kuma jaruma Amrita Singh.

Sara ma 'yar na gada ce gaba da baya, don har kakarta ma wato Sharmila Tagore jaruma ce, haka kanwar babanta Soha Ali Khan ma jaruma ce.

Sara ita ma ta shiga fagen fina-finan Bollywood, kuma za a fara ganinta a fim ne tare da jarumi Sushant Singh Rajput, wato Kedarnath, wanda Abhishek Kapoor ya bayar da umarnin, Ronnie Screwvala kuma ya shirya shi.

Kedarnath fim ne da ya kunshi labarin wata mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a India a baya.

Mahaifin Sara wato Saif, ya ce ya zaku ya ga an saki fim din 'yarsa na farko. Za a saki fim din ne a watan Janairun 2019.

Shekarun Sara a 2018, 24.

4. Karan Deol

Hakkin mallakar hoto The Express Tribune

Karan Deol mai shekaru 27 da haihuwa, shi ne babban da a wajen jarumi Sunny Deol.

Sunny Deol da kansa ya ce lokaci ya yi da dansa zai shiga a dama da shi a fina-finan Indiya, domin shi ma dan na gada ne.

Sunny Deol ya ce da kansa zai bayar da umarnin fim din da dansa Karan zai fara fitowa.

Tuni dai aka fara shirin fim din mai suna Pal Pal Dil Ke Paas.

Jama'a da dama dai sun zaku su ga irin yadda Karan zai taka rawa a wannan fim, kasancewar mahifinsa Sunny ya yi suna wajen fina-finai na fada, to amma shi Karan da fim din soyayya zai fara.

Ba a sanar da ranar da za a saki fim din Karan na farko ba wato Pal Pal Dil Ke Paas.

5. Banita Sandhu

Hakkin mallakar hoto The Express Tribune

Banita Sandhu 'yar asalin kasar Indiya ce mai shekara 20 da haihuwa, amma haifaffiyar birnin Landon.

A Landan ta girma har ta yi karatu, a yanzu haka tana dab da kammala karatun digirinta a King's College, da ke Landan.

Mai tallan kayan kawa ce. Tun tana karama ta ke da sha'awar yin fim irin na kasarsu.

Banita ta yi nasarar shiga fim din "October" wanda suka fito tare da jarumi Varun Dhawan.

October fim ne na wata irin soyayya wanda kuma aka sake shi a watan Afrilun 2018.

Fim ne da Shoojit Sircar ya bayar da umarnin. October ya samu karbuwa sosai a cikin fina-finan da aka saka a 2018.

Yanzu haka Banita Sandhu ta ce ta shiga fagen fim da kafar dama, don kuwa yawancin ma su shirya fim da ma ma su bayar da umarninsa, sun yaba da rawar da ta taka a fim dinta na farko wato October.

6. Utkarsh Sharma

Hakkin mallakar hoto The Express Tribune

Utkarsh Sharma shi ne wanda ya fito a fim din Gadar: Ek Prem Katha a matsayin dan Sunny Deol da kuma Amisha Patel.

Yanzu shi ma ya girma har an fara shirin fim din da zai kasance babban tauraro a ciki wato Genius.

Fim din Genius fim ne soyayya, wanda kuma mahifinsa na gaske Anil Sharma, ya shirya tare da bayar da umarninsa.

Mahaifinsa ya ce yana da yakinin cewa dansa Utkarsh zai yi abin azo a gani a fim din.

Utkarsh zai fito ne tare da Ishitha Chauhan a cikin fim din, za a sake shi a watan Agustan 2018. Shekarun Utkarsh a yanzu 23.

7. Ankita Lokhande

Hakkin mallakar hoto The Express Tribune

An fi sanin Ankita a shirye-shiryen talabijin na kasar wato Series.

Ga ma'abota kallon irin shirye-shiryen talabijin din Indiya da ake nunawa a Zee TV da Zee World da kuma Sony TV, za su iya gane Ankita.

Daga cikin series din da ta fito akwai Pavitra Rishta, wanda ta fito a matsayin Archana.

Yanzu Ankita, za ta koma fitowa a fina-finan Indiya, inda za ta fara da fim Manikarnika.

Labari ne na wata sarauniya da ta yi suna a India.

Za ta fito tare da Kangana Ranaut. Nan gaba kadan cikin 2018, za a saki fim din. Shekarun Ankita 33.

8. Rohan Mehra

Hakkin mallakar hoto The Express Tribune

Da ne a wajen marigayi Vinod Mehra.

Zai fara fim ne tare da Saif Ali khan, wato fim din Bazaar, wanda za a saka a karshen watan Afrilun 2018.

Fim Bazaar ya kunshi labarin kasuwancin hannayen jari. Shekarun Rohan 29.

Abubuwan da masu kallo ke fatan wadannan sabbin taurari za suyi

Wadannan sabbin fuskoki da za a fara gani a fina-finan Indiya, an san iyayensu, don haka ma su kallo ke sa ran su ga sun taka muhimmiyar rawa kamar ta iyayensu koma su fi su.

Sannan kuma, ma su kallo na fatan wadannan sabbin jarumai za su rinka isar da sakon da ake son isarwa a fim yadda ya kamata.

Labarai masu alaka