'Yan sandan Turai sun lalata kafar farfagandar IS

Mayakan IS Hakkin mallakar hoto SCREEN GRAB
Image caption IS tana watsa hotunan bidiyo da dama a fadin duniya ta hanyoyinta na farfaganda

Rundunar 'yan sandan Tarayyar Turai ta ce ta yi gagarumar illa ga kafar watsa farfagandar kungiyar IS, a wani aiki da ta kaddamar ta intanet a fadin kasashe takwas, wanda ta aiwatar da hadin guiwar kawayenta na Amurka ta Arewa.

Shugaban rundunar 'yan sandan ta Turai, Europol, Rob Wainwright, ya bayyana cewa aikin da aka yi a wannan makon bisa jagorancin ofishin mai gabatar da kara na Belgium ya hari musamman kafar watsa labarai ta IS ne, Amaq, wadda ake amfani da ita wajen sanar da cewa kungiyar ta kai wasu hare-hare da dama, idan an kai.

Wannan harin na intanet wanda shi ne na uku da aka kai wa IS, yana da matukar kalubale kan yadda aka tafiyar da shi, saboda akwai tarin hukumomin 'yan sanda da jami'ai da suka yi aiki tare domin kwace rumbunan na'urorin samar da intanet a kasashen da suka hada da Birtaniya da Belgium da Bulgaria da kuma Amurka.

Shugaban rundunar 'yan sandan kungiyar kasashen Turan, ya ce an aiwatar da harin ne bayan aikin tattara bayanan sirri da aka yi na tsawon shekaru, kuma ya ce aikin ya tafi yadda aka tsara shi, domin ya haifar da gagarumin nakasu ga kungiyar ta IS wajen amfani da cibiyar tata ta yada farfaganda wanjen mayar da matasa masu tsattsauran ra'ayi.

Babban jami'in ya ce bayan da aka karya lagon kungiyar ta IS a fagen yaki, yanzu kuma an kassara ta, ta intanet.

Sai dai kuma babban jami'in 'yan sandan ya yi gargadin cewa hakan ba yana nufin kafofin yada farfagandar na IS sun mutu ba ne murus.

Ya kuma kara bayani da cewa yana sa ran za su biyo baya da kamen masu hannu a shafukan watsa farfagandar na IS bayan bata kafofin nata da aka yi.

Labarai masu alaka