Dalilin da ya sa za a yi wa maza 1,000 kaciya

Ba a yi wa maza kaciya a wasu wurare a Mozambique Hakkin mallakar hoto AFP

Za a yi wa maza fiye da 1000 kaciya a Mozambique, a wani mataki na kare yaduwar cututtukan da ake iya dauka a wajen jima'i ciki har da cutar HIV/AIDS.

Jami'an lafiya a tsakiyar lardin Zambezia, sun ce za a yi kaciyar ne a gundumomi kamar na Ato-Molocue da Ile da kuma Gurue, inda ba a yin kaciya a yankunan.

Wannan shi ne karo na biyu da za a yi irin wannan aiki wanda aka fara tun a bara inda aka yi wa maza 84,000 kaciyar a lardin.

Abdul Razak, likita ne kuma shi ne gwamnan Zambezia, daya daga cikin gundumomin da ke da yawan jama'a, ya kuma goyi bayan wannan aiki.

Ya ce "Abin da na ke so na fahimtar da ku shi ne, za a yi kaciyar ne domin kare yaduwar cututtuka kamar HIV, amma yin kaciyar ba ya warkar da wadanda suka kamu da cutar".

Za a kashe kusan dala 7,28000, wajen kaciyar, kuma wata kungiya mai suna US initiative President's Emergency Plan for Aids Relief (Pepfar), ce ta dauki nauyi.

Kaciyar maza ba bakon abu ba ne a wasu yankunan Mozambique ciki har da gundumomin Cabo Delgado, da Niassa, da Tete da kuma Inhambane.

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kaciyar maza na rage yiwuwar kamuwa da cutar HIV da kimanin kashi 60 cikin dari.

Labarai masu alaka