Kun san Daraktocin Indiya da fim dinsu bai taba kwantai ba?

1. Rajkumar Hirani

Hakkin mallakar hoto Bolywood News

Rajkumar Hirani na daga cikin daraktocin fina-finan Indiya da suka samu gagarumar nasara a sana'arsu.

Fim na farko da ya fara bayar da umarninsa shi ne Munnabhai MBBS , wanda aka yi a 2003.

Tun daga nan kuma sai likkafa ta ci gaba, saboda Munnabhai MBBS ya samu karbuwa sosai.

Rajkumar Hirani ya kafa tarihi sosai a Bollywood saboda fina-finai hudu kawai ya bayar da umarninsu, kuma dukkansu sun samu gagarumar nasara da karbuwa.

Fina-finan da Rajkumar Hirani ya bayar da umarninsu:

 • Munnabhai MBBS: Hit
 • Lage Raho Munnabhai: Blockbuster
 • 3 Idiots: All Time Blockbuster
 • PK: All Time Blockbuster

2. Karan Johar

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Karan Johar Matashin daraktan ne wanda kuma ya shigo Bollywood da kafar dama, kasancewar shi ya gaji wannan sana'a ta shirya fim da kuma bayar da umarninsa.

Da farko ya kan taimakawa mai bayar da umarni a fim, daga baya kuma sai ya fara bayar da umarni da kansa.

Fim din Karan na farko da ya bayar da umarninsa shi ne Kuch Kuch Hota Hai a shekarar 1998.

Wannan fim dai har yanzu ana yayinsa saboda kyawun da ya yi. Daga nan kuma sai Kabhi Khushi Kabhi Gham wanda shi ma ya samu karbuwa sosai.

Karan Johar ya kan shirya fim ba bayar da umarni kawai ya ke yi ba, saboda suna da kamfaninsu na shirya fina-finai mai suna Dharma Production.

Kamfanin mahaifinsa ne, da ya rasu kuma sai ya ci gaba da amfani da kamfanin.

Fina-finan da Karan Johar ya bayar da umarninsu

 • Kuch Kuch Hota Hai
 • Kabhi Khushi Kabhi Gham
 • Kabhi Alvida Na Kehna
 • My Name Is Khan
 • Student of The Year
 • Ae Dil Hai Mushkil

Karanta karin wasu labaran

3. Rakesh Roshan

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Rakesh Roshan jarumi ne wanda ya yi tashe shekarun 1970.

Rakesh ya samu shiga sahun daraktoci biyar da suka yi fina-finan da ba su taba faduwa ba, saboda fina-finai bakwai da ya yi tun daga 1995 kawo yanzu.

A baya kafin 1995, fina-finan da ya ke bayar da umarninsu ba su fiye kasuwa ba.

To daga baya ne kuma fina-finan da ya ke bayar da umarninsu suka fara karbuwa.

Rakesh Rosha ya bayar da umarnin fitattun fina-finai da suka tashe sosai kamar Karan Arjun da Kaho na Pyar Hai.

Fina-finan Rakesh Roshan da suka samu karbuwa

 • Karan Arjun
 • Koyla
 • Kaho Na Pyaar Hai
 • Koi Mil Gaya
 • Krrish
 • Krrish 3

4. Ali Abbas Zafar

Hakkin mallakar hoto Bollywood News

Matashin mai bayar da umarni ne saboda shekarunsa 38 da haihuwa. Ya kasance yakan rubuta labarin fim, daga baya kuma sai ya fara bayar da umarni.

Fim din 'Mere Brother Ki Dulhan', shi ne fim na farko da ya fara bayar da umarni, kuma ya samu karbuwa.

Sauran fina-finan da ya bayar da umarninsu akwai Gunday wanda shi ma ya samu karbuwa da Sultan wanda ya samu karbuwa sosai sai kuma Tiger Zindagi Hai.

5. Neeraj Pandey

Hakkin mallakar hoto Bollywood News

Pandey ya kawo wani sabon tsarin sinima a Indiya.

Ba kasafai mukan ga manyan fina-finai da ke nuna rayuwa ta zahiri suna kasuwa ba, amma Pandey ya gwama harkar kasuwanci da zahirin rayuwa- hakan kuma ya zama wani lakani na samun nasara.

Daraktan ya fara bayar da umarni ne a wani fim mai suna "A Wednesday" wanda karbuwarsa ta ba da mamaki, sannan ya biyo bayansa da "Special 26" wanda ya sake samun karbuwa a wajen 'yan kallo.

Sauran fina-finan da Neeraj Pandey ya bayar da umarninsu, kuma suka samu karbuwa, sun hadar da 'Baby' da kuma 'MS Dhoni', wadanda dukkansu sun samu karbuwa sosai a wajen 'yan kallo.

Karin bayani

Akwai sauran masu bayar da da umarnin a fina-finan Indiya da suka samu nasara a sana'arsu, sai dai kuma wasu daga cikin fina-finan nasu ba sa samun karbuwa sosai a wajen 'yan kallo.

Daga cikinsu akwai Aditya Chopra, wanda ya shahara sosai, kuma ya bayar da umarnin fina-finan da suka yi tashe sosai kamar 'Dilwale Dulhania Le Jayenge' da 'Mohabbatein'.

Sai Farhan Akhtar shi ma ya bayar da umarnin fina-finan da suka yi tashe, haka ma Sanjay Leela Bhansali.

Labarai masu alaka