Shadda ta rufta da wasu daliban firamare

Harabar wata masai ke nan a Kenya da dalibai suka fada Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana sheka ruwan sama a 'yan kwanakin nan a kasar Kenya

Rahotanni sun ce wasu yara dalibai su shida da ke karatu a wata makaranta da ke wani kauye a Kenya sun fada cikin masai, bayan da shaddar ta rufta a safiyar ranar Laraba.

Kafar talbijin din kasar ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a yankin Nakuru, da ke arewa maso yammacin babban birnin kasar, Nairobi.

Shaddar ta rufta ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake ta yi a kasar a 'yan kwanakin nan.

Daliban dai 'yan makarantar firamare ne, kuma rahotanni sun ambato shugaban makarantar na cewa, hudu daga cikinsu ba su samu rauni ba.

Amma ya tabbatar da cewa sauran biyun sun jikkata.

To sai dai kuma daga bisani an ceto dukkanin daliban su shida daga cikin shaddar data rufta

Shugaban makarantar frimare ya kuma tabbatar da haka.

Wakiliyar BBC Mercy Juma ta ce iyayaye da masu aikin ceto da kuma sauran jama'a sun hada karfi da karfe wajan tono baraguzan shaddar da ta rufta domin ceto daliban

Labarai masu alaka