Adam Zango ya fitar da bidiyon wakar gambara

Adam A Zango Hakkin mallakar hoto Adam Zango self youtube
Image caption An dade da fitar da wakar gambara amma sai yanzu ne aka saki faifanta na bidiyo

Jarumin fina-finan Hausa kuma mawaki Adam A Zango ya fitar da faifan bidiyon wakarsa ta gambara.

Mawakin ya sanar da haka ne a shafinsa na Instagram, inda ya wallafa kadan daga cikin bidiyon.

A takaitaccen bidiyon mai tsawon minti 3:43 da aka wallafa a shafinsa na YouTube, Zango ya yi zambo kamar yadda aka saba ji a wakokin gambara.

Jarumin ya yi habaici ga wadanda ya ce ba sa son jin wakar Hausa da kuma abokan adawa.

"Wai wakar Hausa ce ba sa so, ba jinja ba suwaga, a gidan chasun garinmu sun fi son Wizkid ko Lady Gaga", in ji Adam A zango.

Mawakin, wanda ke yawon janyo ce-ce-ku-ce, ya ce shi ne ya bayar da umarnin tsara bidiyon sannan ya yi wa kansa kirari.

"Ni magana gadon gidanmu ce, tun [ranar] Litinin idan na fara zan kai Asabar sannan na huta", in ji shi.

Da ma dai tuni aka fitar da wakar, amma sai yanzu ne aka saki faifanta na bidiyo.

Labarai masu alaka