Akalla mutum 30 aka kashe a harin Numan na Adamawa

Maharan sun kona gidaje da dama a kauyukan Bolki da Bang da kuma kauyen Gon a karamar hukumar na Numan Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Maharan sun kona gidaje da dama a kauyuka hudu na yankin Numan

Akalla mutum 30 ne suka hallaka a harin da wasu 'yan bindiga suka kai wasu garuruwa hudu da ke karamar hukumar Numan a jihar Adamawa ta Najeriya.

Shugaban karamar hukumar Numan Reverend Arnold Jibla ya tabbatarwa BBC kai hare-haren.

A cewarsa, maharan sun kona gidaje da dama a kauyukan Bolki da Bang da kuma kauyen Gon a yankin Numan.

Jami'ia sun kuma ce maharan sun afkawa da garuruwan da aduna da bindigogi a yankin na Numan.

Sun dora alhakin harin a kan Fulani makiyaya. Sai dai Fulani ba su ce komai game da wannan batun amma a baya sun sha musanta zargi irin wannan.

Yankin dai ya dade yana fama da rikice-rikicen kabilanci da na addini wanda ake alakantawa da makiyaya da kuma Fulani.

Sai dai kawo yanzu ba bu wata kungiya data dauki alhakin kai harin.

Ko da yake a baya kungiyar Boko Haram ta rika kai hare-hare a yankin.

Wannan harin dai na zuwa 'yan kwanaki bayan harin kunar bakin-wake da aka kai wani masallaci a garin Mubi na jihar ta Adamawa inda aka hallaka mutane da dama.