Jaruman Kannywood na alhinin rasuwar Hauwa Maina

Sakon da Ali Nuhu ya wallafa Hakkin mallakar hoto Instagram/@realalinuhu
Image caption Jarumar ta fito a fina-finai da dama a tsawon rayuwarta

Jaruman fina-finan Hausa na Kannywood suna ci gaba da nuna jimami da alhinin rashin marigayiya Hauwa Maina wadda ta rasu ranar Laraba a Kano.

A sakonnin da suka wallafa a shafukansu na sada zumunta na Instagram, jaruman sun yi addu'ar Allah ya gafarta wa marigayiyar.

Hauwa ta kasance daya daga cikin matan da suka fi dadewa suna fitowa a fina-finan Hausa.

A cikin sakonnin nasu, wasunsu sun saka alamar kuka domin nuna jimami game da rashin jarumar ta Kannywood.

Baya ga haka wasu jaruman kamar mawakin nan Nazifi Asnanic, sun wallafa kadan ne daga cikin fina-finan da ta yi a lokacin da take raye.

Rayuwar Hauwa Maina a takaice

Image caption Hauwa Maina ta rasu bayan ta sha fama da jinya
  • Tun 1999 ta fara fim din Hausa, bayan ta koma garin Kaduna da zama
  • Fim din ta na farko shi ne Tuba wanda Malam Yahya, wani tsohon ma'aikacin gidan talbijin na kasa NTA ya bayar da umarni
  • Ta fara fitowa a matsayin budurwa, sai kuma matar aure, sannan ta koma tana fitowa a matsayin uwa
  • Ita ce ta fito a fina-finai na tarihi kamar Quen Ameena Sarauniyar Zazzau, da Sarauniya Daurama.

A wata hira da ta yi da BBC Hausa da ba a kai ga wallafawa ba, Hauwa Maina ta ce ba kowane irin fim take amincewa ta fito ba.

Ta ce tana fitowa ne kawai a fim din da ta gamsu cewa labarinsa ya yi ma'ana, kuma zai ilmantar.

Tuni dai jarumai na fina-finan Hausa suke ta bayyana alhini dangane da rasuwar jarumar, wacce da dama ke dauka a matsayin uwa.

Bayan fina-finan Kannywood, Hauwa Maina ta kuma fito a fina-finan Nollywood na Kudancin Najeriya da ake yi da Turanci.

Labarai masu alaka