Alex Iwobi na bakin ciki da murna kan tafiyar Arsene Wenger

Nigeria and Arsenal's Alex Iwobi
Image caption Alex Iwobi ya ce fatansu shi ne su lashe gasar Europa saboda Wenger

Dan wasan Najeriya da ke taka-leda a Arsenal, Alex Iwobi, ya ce yana farin ciki da kuma bakin ciki a kan tafiyar kochin kungiyar, Arsene Wenger.

Iwobi ya shaida wa BBC cewa Wenger ne ginshikin sana'arsa ta kwallon kafa wanda ya fara tun yana yaro.

"Abin bakin ciki ne a gare ni. Ya kasance mai ba ni karfin gwiwa. Ya yi mun abubuwa da yawa a harkata ta kwallon kafa, saboda haka ina dan jin bakin cikin tafiyarsa, amma kuma ina jin karsashi kan hakan.

Ba mu san wanda zai shigo ba, muna jira ne kawai," in ji Iwobi.

Iwobi ya ce shi da takwarorinsa na kungiyar Arsenal za su so su yi wa Wenger walimar tafiya ta hanyar cin kofin gasar kofin gasar Europa.

"Ya cancanci walimar tafiya da ta fi dacewa. Saboda haka ya kamata mu yi iya kokarinmu domin mu kammala wannan kakar da karfinmu. Abun da yake so a gare mu shi ne mu gama kakar da karfi kuma mu yi kokarin lashe gasar Europa.

Wannan ita ce kyauta mafi girma da za mu iya ba shi," in ji dan Najeriyar mai shekara 21.

Gunners da Atletico Madrid sun tashi canjaras 1-1 a filin wasa na Emirates.

A daidai lokacin da ake kokarin yin zagaye na biyu na karawar, sai Iwobi da sauran 'yan wasan Arsenal sun matsa kaimi kafin su doke Atletico Madrid a digansu.

Kawo yanzu yanzu dai Atletico Madrid ba ta dandana shan kaye ba a filin wasa na Wanda Metropolitan a gasar La Liga ta wannan kakar.

Chelsea ce kawai ta ka doke ta a gasar zakarun Turai yayin da Sevilla ta doke ta a gasar Copa del Ray.

Za a buga wasan karshe na gasar cin kofin Europa League a birnin Lyon ranar 16 ga watan Mayu.

Labarai masu alaka