Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka a makon jiya

An Zabi hotuna mafi kyau daga ko'ina a Afirka da na 'yan Afirka a wasu wurare a duniya a wannan makon.

Wasu daga cikin 'ya'yan kungiyar kwadago a Afirka ta Kudu ke nan, ke hutawa a bikin zagayowar ranar ma'aikata da aka yi a cikin mako inda suka bukaci a karawa ma'aikata albashi a kasar daga ranar 1 ga watan Mayun 2018 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wasu daga cikin 'ya'yan kungiyar kwadago a Afirka ta Kudu ke nan, ke hutawa a bikin zagayowar ranar ma'aikata da aka yi a cikin mako inda suka bukaci a karawa ma'aikata albashi a kasar daga ranar 1 ga watan Mayun 2018
A wannan ranar kuma, wasu 'yan rawa sun nishadantar da 'yan kallo a lokacin bikin zagayowar ranar ma'aikata a Nairobi, babban birnin kasar Kenya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A wannan ranar kuma, wasu 'yan rawa sun nishadantar da 'yan kallo a lokacin bikin zagayowar ranar ma'aikata a Nairobi, babban birnin kasar Kenya
Sojojin fadar gwamnatin Sudan a tsaye domin jiran isowar firaministan kasar Habasha Khartoum a ranar 2 ga watan Mayu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin fadar gwamnatin Sudan a tsaye domin jiran isowar firaministan kasar Habasha birnin Khartoum
Wata mata tana hada tukunyar kasa a yayin bikin baje kolin jawo hankalin masu yawon bude ido a birnin Abidjan na Ivory Coast a ranar 27 ga watan Afrilu, 2018 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wata mata tana hada tukunyar kasa a yayin bikin baje kolin jawo hankalin masu yawon bude ido a birnin Abidjan na Ivory Coast
A Zimbabwe, wasu mutane ne ke wasan lankwasa jiki domin kayatar da 'yan kallo a lokacin bikin gargajiya na shekara-shekara da ake yi a birnin Harare a ranar 1 ga watan Mayu, 2018 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A Zimbabwe, wasu mutane ne ke wasan lankwasa jiki domin kayatar da 'yan kallo a lokacin bikin al'adu na shekara-shekara da ake yi a birnin Harare
Yayin bikin na shekara-shekara, ana baje kolin al'adu na gida da ma na kasashen waje da suka hada da wasan dabe, da raye-raye, da kade-kade da wake-wake, da kalankuwa, da tufafi, da zane-zane. an yi shi ne a ranar 1 ga watan Mayun, 2018 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Yayin bikin na shekara-shekara, ana baje kolin al'adu na gida da ma na kasashen waje da suka hada da wasan dabe, da raye-raye, da kade-kade da wake-wake, da kalankuwa, da tufafi, da zane-zane
Mahalarta bikin shekara-shekara na Afrikaburn da ake gudanarwa a Tankwa Karoo, Calvinia, a Afirka ta Kudu na nishadi a wani wuri da ake amfani da shi don daukar hoton selfie. a ranar 27 ga watan Afirilun, 2018 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mahalarta bikin shekara-shekara na Afrikaburn da ake gudanarwa a Tankwa Karoo, Calvinia, a Afirka ta Kudu na nishadi a wani wuri da ake amfani da shi don daukar hoton selfie.
Tsohuwar shugabar Malawi, Joyce Banda, ta dauki hoto a filin jirgin saman Chileka da ke Blantyre, bayan da ta dawo gida daga gudun hijira a ranar 28 ga watan Afirilu, 2018 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsohuwar Shugabar kasar Malawi, Joyce Banda, ta dauki hoto a filin jirgin saman Chileka da ke Blantyre, bayan da ta dawo gida daga gudun hijira
Wani sojan Kamaru fuskarsa a daure a yayin da ya ke shirin fita aikin dare a wajen garin Buea da ke cikin yankin Kudu maso yammacin kasar a ranar 26 ga watan Afirilun, 2018 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani sojan Kamaru fuskarsa a daure a yayin da ya ke shirin fita aikin dare a wajen garin Buea da ke cikin yankin Kudu maso yammacin kasar
Sojoji suna yaki da kananan kungiyoyin masu daukar makamar da ke neman 'yanci a kasar Kamaru a bangaren masu amfani da harshen ingilishi da ke iyakar kasar da Najeriya a ranar 26 ga watan Afirilu , 2018. An dai fara wannan rikici ne tun a wtaan Nuwambar 2016, inda lamarin ya yi kamari a Oktoban 2017 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojoji suna yaki da kananan kungiyoyin masu daukar makamai da ke neman 'yanci a kasar a bangaren masu amfani da harshen Ingilishi da ke iyakar kasar da Najeriya
A Tunisiya, wani mutum yana tuka kekensa inda ya wuce wani zane da aka yi a cikin wani wurin shakatawa a tsibirin Djerba, a ranar 1 ga watan Mayun, 2018 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A Tunisiya, wani mutum yana tuka kekensa inda ya wuce wani zane da aka yi a cikin wani wurin shakatawa a tsibirin Djerba

Hotuna daga AFP da Getty da Reuters da kuma EPA

Labarai masu alaka

Labaran BBC