Tarihin marigayiya Hauwa Maina
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tarihin marigayiya Hauwa Maina

A ranar Laraba ta farkon watan Mayu ce Hauwa Maina ta rasu a asibiti a Kano bayan doguwar rashin lafiya.

Ta kwanta a asibitin kasa da ke Abuja, kafin daga baya aka mayar da ita Asibitin Nasarawa da ke Kano inda ta rasu.

Da safiyar Alhamsi ne kuma aka yi jana'izarta a mahaifarta jihar Kaduna, inda kuma a nan ne ta zauna gabanin rasuwarta.

Tauraruwar ta fina-finan Hausa ta rasu tana da shekara hamsin a duniya.